An Damke Chukwudi Da Shuaibu Da Bindigogi 18 Da Harsasai 1,300 Zasu Kai Abuja

An Damke Chukwudi Da Shuaibu Da Bindigogi 18 Da Harsasai 1,300 Zasu Kai Abuja

  • Jami'an tsaro sun kama wasu matafiya biyu dauke da bindigogi goma sha takwas da harsasai sama da 1,300
  • Jami'an NDLEA na binciken motocin ne don duba ko safarar kwaya akai sai suka ci karo da bindigogi
  • An mikasu ga hukumar yan sandan jihar Kogi domin gudanar da bincike kan su da makaman

Kogi - Jami'an hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi NDLEA, a ranar Asabar, 17 ga Satumba sun damke fasinjoji biyu da bindigogin PAP guda 18 da harsasai 1,300 a jihar Kogi, Arewa maso tsakiyar Najeriya.

Leadership ta ruwaito cewa fasinjojin biyu; Chukwudi Aronu, 51, da Shuaibu Gambo, 23,na cikin motar J5 daga Onitsha kuma sun nufi shiga Abuja daga nan su tafi Kaduna.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, bayyana hakan ranar Lahadi.

Yace jami'an sun damkesu ne yayinda suke sintiri a titin Okene-Lokoja-Abuja.

Kara karanta wannan

Surukin tsohon shugaban Najeriya ya shiga hannun EFCC, sun maka shi a kotu saboda zamba

Yace:

"Hakazalika mun sake damke wani Anthony Agada, 37, yana dauke da harsasai 1,000 a cikin motar duk a rana guda ya taso daga Onitsha zai tafi Abuja."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NDLEA
An Damke Chukwudi Da Shuaibu Da Bindigogi 18 Da Harsasai 1,300 Zasu Kai Abuja Hoto: Leadership
Asali: Twitter

An Damke Isyaku da Usman Da Bindigogi 12 Da Harsasai 375 Zasu Kai Abuja

A makonni biyu da suka gabata, mun kawo muku labarin yadda hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi NDLEA, sun damke fasinjoji biyu da bindigogin PAP guda 12 da harsasai 374 a jihar Kogi.

Kamfanin dillancin labarai NAN a ruwaito cewa fasinjojin biyu; Sagir Isiyaka (40) da Bello Shehu Usman na cikin motar J5 daga Onitsha kuma sun nufi shiga Abuja.

Kwamandan hukumar NDLEA na jihar Kogi, Abdulkadir Abdullahi-Fakai, yace jami'an sun damkesu ne yayinda suke sintiri a titin Okene-Lokoja-Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel