‘Yan Bindiga Sun Farmaki Coci, Sun Sace 40, Suna Neman Kudin Fansa N200m
- 'Yan bindiga sun farmaki al'ummar kwatas din Bayan Kasuwa da ke Kasuwan Magani, karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna
- Kungiyar SOKAPU ta bayyana cewa maharan sun yi garkuwa da mutum 40 daga wani coci a yayin da suke tsaka da ibadah
- Shugaban kungiyar, Dr. Awemi Maisamari, ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tubtubi yan uwan wadanda abun ya ritsa da su inda suka nemi a biya miliyan N2
Kaduna - Kungiyar mutanen kudancin Kaduna wato SOKAPU ta yi zargin cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da sama da mutum 40, harda yan coci a kwatas din Bayan Kasuwa da ke Kasuwan Magani, karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr. Awemi Maisamari,ya gabatarwa manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, ya ce yan bindigar sun tuntubi yan uwan wadanda aka sace inda suke nemi a biya naira miliyan 200 kafin su sake su.
A cewar kungiyar, lamarin ya afku ne a ranar 12 da 13 ga watan Satumba, a yankin Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru, yan kilomita daga cikin birnin.
Maisamari ya bayyana cewa har yanzu garuruwan da ke kudancin Kaduna na jihar basu da sukuni domin yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare kan mazauna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Sun ta nakalto yana cewa:
“Har yanzu babu sauran sukuni ga garuruwan da ke kudancin Kaduna. Yan ta’adda, yan bindiga da makiyaya masu makamai suna ci gaba da kai munanan hare-hare garuruwan da ke kudancin jihar.
“Harin baya-bayan nan sune na sace mutane da dama da aka yi a ranar 12 da 13 ga watan Satumban 2022 a Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru na Kudancin Kaduna.
“Kasuwan Magani na kimanin kilomita 20 daga garin Kaduna a kan babban titin Kaduna-Kafanchan da kuma a nan ne babban kasuwan mako na jihar Kaduna yake.
Yan Ta'adda Sun Karbi N19m, Da Kwale-Kwale A Matsayin 'Harajin Tsaro' Daga Mutanen Wasu Garuruwa A Zamfara
“A ranar farko 12 ga watan Satumba, mutum shida aka sace a farmakin dare da yan bindigar suka kai yankin Ungwan Fada da ke garin.
“Ba tare da an dauki mataki don gudun sake faruwar hakan ba, washegari, 13 ga watan Satumba, yan bindigar sun farmaki cocin Cherubim and Seraphim Church, a yayin addu’an dare a kwatas din Bayan Kasuwa da ke garin Kasuwan Magani da tsakar dare.
“Sun yi nasarar dauke fiye da mutum 60 daga cocin da gidajen da ke makwabtaka. Sai dai kuma basu yi nsarar wucewa da dukkansu ba saboda wasun su yara ne sosai, wasu sun tsufa wasu kuma suna da lalura.”
Ya kuma kara da cewa zuwa yanzu an tabbatar da sace mutum 45.
Ya ci gaba da cewa:
“Jiya, 18 ga watan Satumba, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi wasu mutane a garin ta wayar tarho kuma sun yi ikirarin cewa mutum 40 kawai ke tsare a hannunsu.
“Sun bukaci a biya kudin fansa miliyan N200, amma har yanzu ana kan tattaunawa. Bamu san su wanene ba ko makomar mutum biyar da suka bata ba.”
Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Sace Manoma 3 A Kaduna
A wani labarin kuma, mun ji cewa yan bindiga sun yi garkuwa da manoma uku yayin da suka kashe wani mutum daya a garin Kurgin Gabas da ke yammacin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.
Kungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari wato BEPU ta ce tun a ranar 1 ga watan Satumba yan bindiga suka toshe babban titin Birnin-Gwari-Funtua sannan suka kwace motoci fiye da 30 ciki harda manyan motocin daukar kaya, The Nation ta rahoto.
Kungiyar BEPU a cikin wata sanarwa da shugabanta, Ishaq Usman Kasai ya saki, ta kuma bayyana cewa matafiya da dama da aka sace a ranar 1 ga watan Satumba har yanzu ba a sako su ba.
Asali: Legit.ng