Jirgin Sojin Najeriya Ya Kai Sabon Samame Mafakar Bello Turji a Zamfara

Jirgin Sojin Najeriya Ya Kai Sabon Samame Mafakar Bello Turji a Zamfara

  • Jirgin yaƙin NAF ya sake komawa a karo na biyu cikin awanni 48 ya kai samame mafakar kasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji
  • Rahoto ya nuna cewa da safiyar yau Litinin da misalin ƙarfe 9:00 na safe, Jirgin ya saki aƙalla bama-bamai biyu a sansanin
  • Haka nan wani mazaunin Shinkafi a Zamfara yace yan bindiga sun tare matafiya a hanyar Sakkwato zuwa Gusau

Zamfara - Jirgin yaƙin rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya kai sabon hari sansanin ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, a jihar Zamfara.

Daily Trust ta ruwaito cewa ƙasurgumin ɗan ta'addan ya tsallake rijiya da baya a wani harin ruwan bama-bamai da sojoji suka kaddamar a gidansa ranar Asabar.

Jirgin yakin sojin Najeriya.
Jirgin Sojin Najeriya Ya Kai Sabon Samame Mafakar Bello Turji a Zamfara Hoto: NAF
Asali: UGC

Wata majiya ta shaida mana cewa Jirgin ya sake koma wa wurin da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar yau Litinin, ya saki aƙalla bama-bamai guda biyu.

Kara karanta wannan

Kyakkyawan Karshe: Malamar Makaranta Ta Mutu Tana Tsaka Da Karatun Al-Qur'ani

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a kwanakin baya, gwamnatin Zamfara ta yi ikirarin cewa Bello Turji, ya rungumi shirin zaman lafiya da gwamnatin Matawalle ta zo da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan ta'adda sun tare babbar hanya

A halin yanzun, wasu yan bindigan daji da ake kyautata zaton mayaƙan Bello Turji ne sun kai hari kan matafiya a babban titin Sakkwato zuwa Gusau, a ƙaramar hukumar Shinkafi.

Wani mazaunin garin Shinkafi, Murtala Wadatau, yace yan ta'addan sun toshe hanya a Kwanar Badarawa da Birnin Yero da safiyar Litinin ɗin nan.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnati ta yi ikirarin cewa ta samu galaba kan taɓarɓarewar tsaron da aka sha fama da shi a sassan Najeriya.

Gwamnatin ta bakin ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, tace duk da akwai sauran yaƙi, amma sojoji sun samu nasarori da dama kan 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Taron Gangamin UN: Hotunan Da Bidiyon Shugaba Buhari Yayinda Ya Isa Birnin New York Cikin Dare

A wani labarin kuma kun ji cewa An Kama Sojan Bogi da Wani Ƙasurgumin Dan Bindiga, Umar Namaro, a Jihar Zamfara

Rundunar yan sanda ta kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga da hatsabiban infoma a ƙoƙarinta na kawo karshen ayyukan ta'addanci a jihar dake arewa maso yammacin Najeriya.

Dakarun sun kama Sojan bogi, da wasu masu da ake zargi da kaiwa yan bindiga Bindigu, Alburusai, Babura, kayan abinci da Kakin sojoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262