Dalilin Da Yasa Har Yau Yan Bindiga Ke Amfani da Layuka Duk da Hada NIN-SIM, Pantami

Dalilin Da Yasa Har Yau Yan Bindiga Ke Amfani da Layuka Duk da Hada NIN-SIM, Pantami

  • Sheikh Farfesa isa Ali Pantami yace har yanzun yan ta'adda na amfani da kiran waya wajen neman kudin fansa duk da haɗa NIN-SIM
  • Sai dai Ministan ya jaddada cewa an samu cigaba sosai a ƙoƙarin shawo kan lamarin tun bayan ɗaukar matakin haɗa layuka da katin ɗan ƙasa
  • Pantami yace bai kamata mutane su yi tsammanin sabon abu ya magance sheɗanci a dare ɗaya ba, sai a hankali a hankali

Abia - Gwamnatin tarayya ta tura sako ga yan Najeriya game da ayyukan 'yan ta'adda duk da matakin haɗa layukan wayoyi da lambar katin ɗan ƙasa (NIN).

Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Sheikh Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya yi ƙarin haske kan lamarin da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: An Kama Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Sojan Bogi a Jihar Zamfara

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isah Pantami.
Dalilin Da Yasa Har Yau Yan Bindiga Ke Amfani da Layuka Duk da Hada NIN-SIM, Pantami Hoto: Isa Pantami/facebook
Asali: Facebook

Ministan yace duk da har yau masu garkuwa da 'yan ta'adda na amfani da waya wajen neman fansa amma an samu ci gaba a kokarin magance lamarin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Pantami ya yi wannan jawabin ne a Umuahia, babban birnin jihar Abiya a wurin taron bikin ranar katin ɗan ƙasa ta duniya 'World National Identity Day.'

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace bai kamata mutane su yi tsammanin rana ɗaya sabon tsarin zai magance sheɗancin ba, inda a cewarsa abu ne da za'a bi mataki-mataki.

A kalamansa, Pantami yace:

"Lamarin 'yan bindiga su kira ta wayar salula domin neman kuɗin fansa ya ragu. Tsaftace matsalar ba zai yuwu a dare ɗaya ba, abu ne da ake bin mataki bayan mataki."
"Waɗannan kiraye-kirayen 'yan damfara 419 sun ragu matuƙa saboda mafi yawan layukan waya an haɗa su da NIN, akwai bukatar lokaci kafin kammala tsaftace tsarin baki ɗaya."

Kara karanta wannan

Ruwan Wuta: Jirgin Yakin Soji Ya Halaka Bashir Iblis da Wasu Ƙasurguman Yan Ta'adda a Arewa

"Amma an samu cigaba matuka gaya, aƙalla zan iya cewa a karon farko, mafi yawan mutane na tsoron aikata abubuwan da lambobin wayarsu."

Na sha fama da barazanar kisa - Pantami

A wani labarin kuma mun kawo muku Yadda Kujerar Minista Ta Jawowa Isa Ali Pantami Barazanar Kisa a Najeriya

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami yayi bayanin kalubalen da ya fuskanta saboda ya kawo tsarin NIN.

A ranar Juma’a 16 ga watan Satumba 2022, Daily Trust ta rahoto Isa Ali Ibrahim Pantami yana cewa ya fuskanci barazanar kisa a kujerar Minista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel