Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Sace Manoma 3 A Kaduna
- Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da wasu manoma uku yayin da suka kashe mutum daya a garin Kurgin Gabas da ke jihar Kaduna
- Kungiyar BEPU ta koka kan yadda yan bindiga suka toshe babban titin Birnin-Gwari-Funtua tun a farkon watan Satumba
- Ta nemi a turo karin sojoji domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da kwatowa direbobi motocinsu da yan bindigar suka tsare
Kaduna - Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da manoma uku yayin da suka kashe wani mutum daya a garin Kurgin Gabas da ke yammacin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.
Kungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari wato BEPU ta ce tun a ranar 1 ga watan Satumba yan bindiga suka toshe babban titin Birnin-Gwari-Funtua sannan suka kwace motoci fiye da 30 ciki harda manyan motocin daukar kaya, The Nation ta rahoto.
Kungiyar BEPU a cikin wata sanarwa da shugabanta, Ishaq Usman Kasai ya saki, ta kuma bayyana cewa matafiya da dama da aka sace a ranar 1 ga watan Satumba har yanzu ba a sako su ba.
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Wani al’amari mai ban damuwa shine cewa yan bindiga sun yi awon gaba da dukka kayayyakin da ke cikin motocin da suka tsare kuma an tilastawa mutane biyan makudan kudade daga N300,000 zuwa naira miliyan 1 domin karbo motocinsu da ke garkame.”
Kungiyar ta kara da cewa yan bindigar sun caji kudi a hannun masu motocin, iya girman motarka, iya yawan kudin da za ka biya, rahoton Punch.
Ya kara da cewa:
“Don haka BEPU na roko da a tura dakarun sojoji don tabbatar da bude hanyar Birnin-Gwari-Funtua da kuma dawo da motocin da aka tsare.”
Yan Bindiga Sun Toshe Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Matafiya Da Dama
A baya mun kawo cewa, yan ta’adda sun toshe hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua, a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
A yayin harin, maharan sun kashe akalla mutum biyu ciki harda wani direba yayin da suka sace mutane da dama.
Hakan ya kasance ne bayan GOC Division 1 na rundunar sojoji, Kaduna, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya jagoranci dakaru da suka kai samame kan yan ta’adda a yankunan Birnin Gwari rahoton The Nation.
Asali: Legit.ng