Dukkan Yan Bindigan Da Aka Kama A Anambra Yan Kabilar Ibo Ne, In Ji Gwamna Soludo

Dukkan Yan Bindigan Da Aka Kama A Anambra Yan Kabilar Ibo Ne, In Ji Gwamna Soludo

  • Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya ce dukkan yan bindigan da aka kama a jiharsa yan kabilar Ibo ne
  • A yan watannin baya-bayan nan, yan bindiga sun rika kai wa jami'an tsaro, mutanen gari da gine-ginen gwamnati hare-hare
  • Soludo ya ce bata garin sun fi zuwa jiharsa ne saboda Anambra ce ta fi arziki a jihohin kudu maso gabas amma gwamnatinsa ta fara magance matsalar

Anambra - Chukwuma Soludo, gwamnan Jihar Anambra, ya ce dukkan yan bindigan da aka kama a jihar kawo yanzu yan asalin yankin kudu maso gabas ne, The Cable ta rahoto.

Soludo, ya bayyana hakan ne lokacin da aka yi hira da shi a shirin Sunday Politics, a gidan talabijin na Channels TV.

Yan bindiga
Soludo: Dukkan Yan Bindigan Da Aka Kama A Anambra Yan Ibo Ne. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

A watannin baya-baya nan, yan bindiga sun rika kai wa mutane, jami'an tsaro da gine-ginen gwamnati hari.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Sace Manoma 3 A Kaduna

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar 11 ga watan Oktoba, yan bindiga sun kai wa tawagar Ifeanyi Ubah, sanata mai wakiltar Anambra ta kudu hari a Nkwo Enugu Ukwu, karamar hukumar Njikoka a Anambra.

An kashe yan sanda da wasu cikin hadiman sanatan.

Gwamnan Anambra ya bayyana ko su wanene 'unknown gunmen'

Da aka bukaci ya yi tsokaci kan maharan da ake kira 'yan bindiga da ba a san su ba', gwamnan ya ce an san su.

Ya ce:

"Bata gari ne, ba wani abu ba."
"Riba ne da bautan gumaka. Wannan sune abubuwa biyu da ke basu kwarin gwiwa.
"Ba bu shakka Anambra ce jihar da ta fi arziki a kudu maso gabas. Don haka, a nan ne aka fi samun kudi mai yawa idan an yi garkuwa da mutane. Don haka, an fi samun laifukan a nan.

Kara karanta wannan

Gwamna Soludo ya Wanke Fulani, Ya Bayyana Wadanda ke Assasa Rashin Tsaro a Anambra

"An san yan bindigan. Ba a san su bane kafin a kama su nan take bayan aikata laifin, amma zan iya tabbatar maka mun rika kama da dama cikinsu kuma sun san wani abu na faruwa kuma ba za su cigaba da cin karensu babu babbaka ba.

Ya cigaba da cewa:

"Bari in fito fili in fada maka. Dukkan mutanen da muka kama yan kabilar ibo ne. Babu wani da ke kawo mana hari daga wani wuri. Kashi dari bisa dari Ibo ne.
"Kashi na farko da muka kama dari bisa dari ibo ne daga wasu jihohin kudu maso gabas amma babu dan Anambra.
"Da muka cigaba, mun gano matasa da yawa cikin wadanda suka koma daji suka shiga irin wannan harkar mazauna jihar Anambra ne ko yan asalin Anambra."

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa na yin duk abin da za ta iya domin magance bata gari a jiharsa.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: An Kama Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Sojan Bogi a Jihar Zamfara

Ya ce an fara samun 'zaman lafiya' domin gwamnatinsa tunda ta fara aiki ta mayar da hankali wurin kawar da bata gari.

Abun bakin ciki: Yan bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Anambra

A wani labarin, wasu tsagerun yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Emeka Alaehobi, a jihar Anambra.

An tattaro cewa an kashe Alaehobi ne a garin Utuh da ke karamar hukumar Nnewi ta kudu a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164