'Yan Ta'adda 29 Sun Mutu Yayi Wata Mummunar Arangama Tsakanin Boko Haram da ISWAP
- Mayakan ta'addanci 29 sun sheka lahira sakamakon mummunar arangama tsakanin ISWAP da Boko Haram
- An gano cewa, mayakan ISWAP sun kai samamen har maboyar 'yan Boko Haram karkashin jagorancin Ba'ana Chigari
- 'Yan Boko Haram sun gaggauta yin taro tare da shan alwashin daukar fansa inda suka tura mayaka yankunan Mafa, Karkut, Shiwai, Lawe, Kanuriye, Kirwa da Amtifur.
Borno - Mayakan kungiyar ISWAP a daren Juma'a sun yi arangama da 'yan ta'addan Boko Haram a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
ISWAP wani tsagi na Boko Haram da suka ware tare da kafa kungiyarsu bayan an samu hargitsin shugabanci. Abubakar Shekau, shugaban Boko haram ya sheka lahira bayan arangamarsu da ISWAP a 2021.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda Zagazola Makama, kwararre a yaki da ta'addanci ya bayyana, 'yan ta'adda 29 sun rasa rayukansu sakamakon arangamar a Borno.
Wasu mayakan ISWAP da suka samu shugabancin Ba'ana Chigori sun kai samame maboyar Boko Haram dake Gaizuwa inda aka fi sani da Gabchari, Mantari da Mallum Masari, wanda hakan ya janyo artabun sa'o'i har zuwa safiyar Asabar.
Wani jami'in sirri ya sanar da Zagazola Makama cewa an yi wa 'yan Boko Haram harin kwantan bauna.
"'Yan ta'addan ISWAP sun fi karfin kungiyoyin hamayyar wadanda suka dira wa ba-zata, kuma an halaka da yawa daga cikinsu yayin da wasu suka race cikin daji don gudun mutuwa."
- Jami'in yace.
“An sassautawa mata da kananan yara.
“Mamatan mayakan an birne su wurin gidan Abu Ikilima dake Gabchari wurin karfe 8:30 na safe a ranar Asabar.
"Shugabannin Boko Haram sun yi taro wurin karfe 11 na safe domin kaddamar da harin daukar fansa kan mayakan ISWAP inda aka aike mayaka Mafa, Karkut, Shiwai, Lawe, Kanuriye, Kirwa da Amtifur."
Wannan cigaban na zuwa ne bayan kwanaki kadan da mayakan ISWAP suka kai harin ba-zata kan mayakan Boko haram a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Bulabuduwaye, Shugaban Masu Zartarwa na Boko Haram da Iyalansa ya Tuba, Ya Mika Wuya Wurin Soji
A wani labari na daban, shugaba masu zartarwa na Boko Haram, Bashir Bulabuduwaye, wanda ke da alhakin yanka dukkan wadanda aka yi garkuwa da su a karkashin umarnin kungiyar, ya mika kansa hannun rundunar sojin Najeriya.
Ya mika wuya tare da iyalansa da suka hada da matansa da 'ya'yansa.
Asali: Legit.ng