An Kama Sojan Bogi da Wani Ƙasurgumin Dan Bindiga a Jihar Zamfara
- Yan sanda sun ce sun kama wani babban ɗan bindiga da ya addabi mutane, Umar Namaro, a jihar Zamfara
- Muhammed Shehu, kakakin yan sandan jihar yace dakaru sun kama wani Sojan Bogi ɗauke da muggan makamai a jihar
- Jami'an tsaro sun sami waɗan nan nasarori ne a kokarinsu na ganin zaman lafiya ya dawo a jihar da ke arewa maso yamma
Zamfara - Rundunar yan sanda ta kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga da hatsabiban infoma a ƙoƙarinta na kawo karshen ayyukan ta'addanci a jihar dake arewa maso yammacin Najeriya.
Channels tv da ruwaito cewa dakarun sun kama Sojan bogi, da wasu masu da ake zargi da kaiwa yan bindiga Bindigu, Alburusai, Babura, kayan abinci da Kakin sojoji.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Muhammad Shehu, shi ne ya bayyana haka yayin nuna waɗanda ake zargin a Hedkwatar 'yan sanda dake Gusau.
Ya ce yan ta'adda sun shiga hannu ne bayan samun kwarararan bayanan sirri da kuma aikin kai samame da jami'ai suka gudanar da mafakar 'yan bindiga a Gusau da ƙaramar hukumar Tsafe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Shehu, dakaru sun kwato bindiga, Kakin Soja, Katin shaida na bogi da wasu makamai masu haɗari daga hannun Sojan Bogi mai suna Zainu Lawal.
"A ranar 14 ga watan Satumba, 2022, dakaru na musamman suka ɗauki matakin kan wasu bayanann sirri da aka tattara game da ayyukan waɗanda ake zargi kamar yadda aka ambata a baya," inji Kakakin yan sanda.
"Wanda ake zargin wanda ya yi ikirarin cewa tsohon Soja ne, ya shiga hannu ɗauke da bindiga, Kakin Soja, Katin shaida na ƙarya da sauran makamai masu haɗari."
An kama kasurgumin ɗan bindiga
Muhammed Shehu ya ƙara da cewa sun kama Umar Namaro, wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mazauna ƙauyukan Mada, Kotorkoshi, da kai hare-haren ta'addanci.
"A ranar 16 ga watan Satumba, dakarun yan sanda yayin Sintiri a hanyar Gusau-Kotorkoshi-Mada suka kama ɗan bindigan. Yayin bincike ya amsa laifinsa."
A wani labarin kuma Gaskiya Ta Fito Kan Ƙishin-Ƙishin Ɗin Tukur Mamu Ya Fallasa Masu Ɗaukar Nauyin 'Yan Ta'adda a Arewa
Mun gudanar da binciken gano gaskiya kan wani rubutu da ake yaɗawa a Facebook da wasu kafafen sada zumunta kan Tukur Mamu.
Rubutun dai ya yi ikirarin cewa mai shiga tsakanin yan ta'adda da FG don sako Fasinjojin jirgin Kaduna ya fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng