Jigawa: Yadda Yan Sanda Suka Ceci Wasu Mutane 7 Da Ake Daf Da Birne Su Da Ransu

Jigawa: Yadda Yan Sanda Suka Ceci Wasu Mutane 7 Da Ake Daf Da Birne Su Da Ransu

  • Da rabon wasu mutane bakwai a garin Bursali za su cigaba da shakar iskar rayuwa bayan da gini ya rufta musu ya danne su kuma mutanen gari suka ceto su amma ba su numfashi
  • Mutanen gari sun shirya tsaf za su birne mutanen bakwai da aka ciro su ba su numfashi daga baraguzan ginin amma yan sanda suka ce dole a kai asibiti a tabbatar
  • Cewa a kai mutanen asibiti a tabbatar da mutuwarsu ya janyo zazzafan jayayya tsakanin yan sanda da yan uwansu amma daga karshe yan sanda suka yi nasara kuma da zu asibit likita ya ce dukkansu bakwai suna da rai

Jigawa - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Jigawa a hana mutanen gari a karamar hukumar Birniwa birne wasu mutum bakwai da ransu, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Ruwa: Mutum 92 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Gwamna Ya Lula Yawon Shakawata Ketare

An gano cewa an yi jayayya tsakanin yan sanda da iyalan mutanen bakwai wanda gini ya rufta musu a kauyen Bursali a karamar hukumar Birniwa.

Taswirar Jigawa
Yan Sanda Sun Ceci Wasu Mutane 7 Da Aka Daf Da Birne Su Da Ransu A Jigawa. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Mutanen kauyen sun ceto wadanda abin ya faru da su kuma suna shirin musu jana'iza.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin yan sandan Jihar Jigawa DSP Lawal Shiisu Adam ya ce:

"Wani ginin kasa a Bursali ya rufta kan wasu mutane bakwai suka makale.
"Da samun labarin, an tura tawagar yan sanda zuwa wurin da abin ya faru. Da isarsu, sun ga mutum bakwai ba su numfashi da guda daya wanda ya jikkata sosai."

DSP Shiisu ya ce mutanen garin sun fara shirin birne wadanda ake ciro ba su numfashi yayin da yan sanda suka dage sai an kai su asibiti an tabbatar.

"Yan sandan sun dage cewa sai an tafi asibiti an tabbatar. Bayan jayayya mai zafi, yan sandan suka yi nasara aka kai su babban asibitin Birniwa.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Neja, Sun Halaka Rayukan Bayin Allah

"Da isarsu asibitin, likita ya duba su ya ce dukkan mutanen bakwai da aka ce sun mutu suna da rai.
"Har ta kai ga hudu daga cikinsu sun fara iya magana a asibitin."

Sanawar da kakakin yan sandan ya fitar ta yi kira ga mutane su rika kyale jami'an tsaro su yi aikin da doka ta dora musu.

An kama sojan gona da kayan hukumar FRSC dauke da katin shaidar aikin soja a Kano

A wani rahoton, jami'an hukumar, FRSC, da hukumar yan sanda sun kama wani mutum mai suna Injiya Gude Ude a jihar Kano da kayan jami'an hukumar kiyaye hadura FRSC kuma dauke da katin shaidar aikin sojan a garin Kano.

Sanarwan da FRSC ta bayar mai dauke ta sa hannun mukadashin Secta Kwamanda, Ahmed T. Mohammed ta ce an kama Ude ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairun 2018 a titin Kaduna - Kano a yayin da rundunar ke gudanar da wata kewaye na musamman da akayi wa take da "Operation Zero".

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Fashe a Babban Birnin Jihar Arewacin Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164