Da Duminsa: 'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

Da Duminsa: 'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

  • 'Dan China ya sokawa budurwarsa mai shekaru 23 wuka inda ta sheka lahira a kwatas din Janbulo na karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano
  • Lamarin ya faru wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan saurayin ya kai wa UmmuKulsum ziyara har gidan iyayenta, duk da ba a tattaro abinda ya hada su
  • 'Dan uwan mamaciyar ne ya hana jama'a kaddamarwa da 'dan China hukunci inda ya kwace shi tare da mika shi hannun 'yan sanda

Kano - Wani mutun 'dan kasar China ya sokawa budurwarsa mai shekaru 23 wuka inda ta mutu a take a kwatas din Janbulo dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Lamarin ya faru ne wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan wanda ake zargin ya kai wa budurwa mai suna UmmaKulsum Sani Buhari ziyara a gidan iyayenta dake kusa da ofishin National Environmental Standards and Regulations Enforcement Agency (NESREA).

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan China a Kano ta yi martani kan kisan da dan China ya yiwa budurwarsa a Kano

'Dan China
Da Duminsa: 'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da abinda ya hada masoyan biyu har yanzu ba a gano shi ba, Daily Trust ta tattaro cewa likitoci sun tabbatar da mutuwar budurwar.

Abubakar Mustapha, wanda makwabci ne ga mamaciyar, ya sanar da Daily Trust cewa bazawara ce kuma wanda ake zargin saurayinta ne.

"Lamarin ya auku wurin karfe 10 na daren da ya gabata. Makashin saurayinta ne tun kafin ta yi auren farko.
"Mijinta ya saketa kuma sun cigaba da soyayyarsu. Yana zuwa gidansu. An kai ta asibitin UMC Zhair wanda bai ka nisan kilomita daga gidansu ba.
“Khaleed, 'dan uwanta shi ya hana jama'a far wa wanda ya kasheta bayan da ya dawo motarsa lokacin da ya shiga gida ya fito. Ya yi tunanin hakan zai janyo wani abu daban. An kama mutumin tare da mikawa 'yan sanda."

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Ɗan China Ya Faɗi Babban Dalilin da Yasa Ya Kashe Budurwarsa Ummita a Kano

- Mustapha yace.

Wani makwabcinsu mai suna Muhammad Sani, ya sanar da cewa wanda ake zargin ya taba yunkurin halaka kansa saboda budurwar amma da taimakon 'yan sanda aka kwantar da tashin-tashinar.

"A lokacin da zata yi aure, ya taba yunkurin halaka kansa saboda soyayyar da yake mata har sai da 'yan sanda suka shiga lamarin sannan aka shawo kansa," yace.

Ya kara da cewa, wanda ake zargin an kai shi ofishin 'yan sanda dake kwatas din Dorayi.

Mamaciyar wacce aka fi sani da Ummita ta yi makarantar koyon jinya da ungozoma dake jihar Kano.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da yin alkawarin samar da karin bayani daga baya.

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da wani wanda ya bayyana sunansa da Aliyu, mazaunin Janbulo a jihar Kano, yace ya san marigayiya Ummita farin sani.

"Mutum ce mai mu'amala mai kyau da jama'a. Suna kawance da kanwata amma aure ya dauke kanwata zuwa garin Jos shiyasa kawancen yayi sauki ba kamar a baya ba.

Kara karanta wannan

Mutum 19 Sun Kone Kurmus A Mumunan Hadarin Mota a Abuja

"A gaskiya mun ji zafin mutuwarta sosai. Komai ta yi wa wannan bakon hauren, bata cancanci irin wannan mutuwar ba. Muna fatan gwamnati da duk hukumomin da suka dace zasu ffi khadin jinin Ummita. Allah yayi mata gafara."

- Aliyu yace.

Yadda ‘Dan China Ya Yaudari Ummita Kan Shiga Musulunci inji Babbar Kawar Marigayiya

A wani labari na daban, wata kawar Ummukulsum Sani Buhari wanda aka fi sani da Ummita, tayi karin haske a kan alakar mai rasuwar da masoyinta, Geng Quanrong. Rabia N.

Garba wanda ta bayyana kan ta a matsayin aminiyar Marigayiyar, ta shaidawa Daily Trust abin da ya wakana tsakanin kawarta da Quanrong.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: