Matashin Da Ya Koma Jami'a Ya Nemi A Biya Shi Kudin Makarantarsa Ya Nuna Abinda Ya Siya Da N500k Da Aka Bashi

Matashin Da Ya Koma Jami'a Ya Nemi A Biya Shi Kudin Makarantarsa Ya Nuna Abinda Ya Siya Da N500k Da Aka Bashi

  • Matashin Da Ya Koma Jami'a Ya Bukaci A Biya Shi Kudin Makarantarsa Ya Nuna Abin Da Ya Siya Da N500,000 Da Aka Bashi Kyauta
  • Oludare Alaba ya ce ya yi amfani da kudin da tsaffin daliban Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola, LAUTECH suka bashi don siyan kayayaki da ya ke bukata don aikinsa
  • Tsohon daliban na LAUTECH, saboda damuwa da ya shiga, ya tafi tsohuwar makarantar ya mayar da takardan karatunsa ya ce a mayar masa kudin da ya biya kafin kungiyar tsaffin daliban ta shiga tsakani

Facebook - Alaba a yanzun ya samu dalilin yin murmushi, ya kuma yi kira ga yan Najeriya su tuntube shi idan suna bukatar mai barkwanci ko mai jagoranci a wurin taronsu.

Rayuwar Oludare Alaba, dalibin da ya kammala Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) wanda ya so mayar da takardar kammala karatunsa don a dawo masa da kudin makarantar ta canja.

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya: "Ba Kan Tinubu Farau Ba Kowa Da Matsalar Shi", Jigon APC Ya Yi Martani Mai Zafi

Mr Alaba
Matashin Da Ya Koma Jami'a Ya Nemi A Biya Shi Kudin Makarantarsa Ya Nuna Abinda Ya Siya Da N500k Da Aka Bashi Kyauta. Hoto: Photo credit: Oludare Alaba.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alaba, wanda saboda bacin rai da damuwa bisa rashin aikin yi, ya tafi jami'ar domin ya mayar da takardar kammala karatunsa a mayar masa da kudin makaranta da ya biya.

Kungiyar tsaffin dalibai na jami'ar mallakar jihar Oyo, amma, ta shiga tsakani, ta bawa Alaba kyautan kudi har N500,000.

A wani bidiyo da ya wallafa a Facebook ranar Laraba, 14 ga watan Satumba, Alaba ya miki godiyarsa ga kyautan da kungiyar ta masa, ya ce ya yi amfani da kudin ya siya kayan da ya ke bukata na aikinsa matsayin mai barkwanci da MC.

An hangi alaba a cikin bidiyon dauke da kwamfuta ta Laptop da wasu kwalaye kanana guda biyu (da ake zaton wayar salula ce da na'urar sauraro)

Tsohon dalibin na LAUTECH ya kuma yi amfani da damar don yin kira ga yan Najeriya su rika gayyatarsa idan za su yi biki idan suna bukatar mai barkwanci ko MC.

Kara karanta wannan

Buhari ya magantu, ya ce akwai wadanda ya kamata suke tallata gwamnatinsa amma ba sa yi

A shafinsa na Facebook, Alaba ya bayyana kansa a matsayin mai barkwanci kuma MC, wato mai jawabi a wurin taruruka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164