Zaben 2023: Ku Zabi Wadanda Suka Fara Yi Muku Aiki Suka Gaza, El-Rufai Ya Fadi Dalili

Zaben 2023: Ku Zabi Wadanda Suka Fara Yi Muku Aiki Suka Gaza, El-Rufai Ya Fadi Dalili

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya shawarci yan Najeriya kan shugabannin da ya kamata su zaba gabannin zaben 2023
  • El-Rufai ya bukaci al'ummar kasar da su zabi wadanda suka yi kokarin magance matsalolinsu koda kuwa basu magance su ba don sun fi wadanda suka haddasa su
  • Ya jinjinawa hukumomin tsaro a kan yadda suka kaddamar da hare-hare kan yan ta'adda da makiyan jihar Kaduna

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa munanan hare-haren da sojoji ke ci gaba da kaiwa kan yan ta’adda da makiyan jihar zai kare Kaduna.

El-Rufai wanda ya yi jawabi a taron kaddamar da littafin Kaduna na 4, ya jinjinawa kokarin hukumomin tsaro wajen maganin masu aikata laifuka a jihar.

Kara karanta wannan

Babu Wani Kulumboto da Sihiri da APC Zata yi Amfani da Shi Don Cin Zabe, Ortom

El-Rufai
Ku Zabi Wadanda Suka Yi Yunkurin Magance Matsalolinku Koda Basu Magance Su Ba, El-Rufai Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan na Kaduna ya bukaci al’ummar kasa da su zabi shugabannin da za su magance matsalolinsu.

El-Rufai ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ku zabi wadanda suka yi yunkurin magance matsalolinku koda basu magance su ba sunfi wadanda suka haifar da su.
“Mun yi nadama cewa saboda lamarin jirgin kasa, har yanzu babu jirgin kasan Abuja-Kaduna, amma a cikin makonni shida da suka gabata, an samu ci gaba a farmakin da ake kaiwa wadannan miyagun kuma muna da karfin gwiwa idan aka ci gaba, a lokacin da za ku dawo taron KABAFEST 5, za ku tuko motarku zuwa Kaduna ba tare da kowani tsaro ba ko daukar jirgin kasa.”

Gwamnan ya yi godiya ga wadanda suka shirya taron, yana mai cewa KABAFEST na da muhimmanci din nuna farin Kaduna sabanin abun da mutane ke fadi game da jihar.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

El-Rufai ya kuma ce burinsa shine ganin cewa Kaduna ya zama inda kowa zai ji tamkar yana a gida ne, babu fifiko ga asalin yan jiha, kabila ko addini, rahoton The Guardian.

A cewarsa, abun da ya kamata asa a gaba shine mutuntawa kowa, ta yadda duk wanda ya zabi rayuwa, zama da biyan haraji zai zama dan Kaduna.

Ya kara da cewa:

“Abin da ya kamata shi ne sanya kowa a zuciya, ta yadda duk wanda ya so zai zauna, ya yi aiki da kuma biyan haraji a matsayin dan Kaduna saboda makomar Kaduna tana hannun matasa, musamman mata, kuma mun kuduri aniyar ba su damar samun ci gaba."

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

A wani labarin kuma, shugaban kungiyar Young Professionals of Nigeria (YPN), Fasto John Desmond, ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Dira Jihar Imo Don Kaddamar Da Wasu Manyan Ayyuka

Desmond ya yi kira ga yan Najeriya da su zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa a babban zaben 2023 mai zuwa.

Ya yi kiran ne Umuahia, jihar Abia, yayin wani rangadi na wayar da kan matasan kungiyar YPN wadanda suke mambobin APC a fadin kudu maso gabas, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng