'Yan Sanda Sun Ceto Wata Uwa da Danta da Tsageru Suka Sace a Jihar Kwara
- Rundunar 'yan sanda ta ceto wata mata da danta da 'yan bindiga suka sace a jihar Kwara a jiya 13 ga watan Satumba
- An kama wasu 'yan bindiga biyu bayan jikkata su, daga baya an samu labarin mutuwarsu a wani asibiti
- 'Yan ta'adda sun addabi Arewacin Najeriya, lamarin da ke kara sanya tsoro a zukatan mazauna yankin
Jihar Kwara - Rahoton Premium Times ya ce, ‘yan sanda a jihar Kwara sun ceto wata mata da danta da aka sace bayan wani dauki ba dadi tsageru a wani aikin ceto da ‘yan sanda, 'yan banga da mafarauta suka yi.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandamn jiharr, Okasanmi Ajayi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Ilorin.
A cewar sanarwar:
"A ranar 13 ga Satumba, da misalin karfe 11:20 na dare, an sace Afusat Lawal da danta, Taofeek Lawal, aka tafi da su."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ajayi ya ce an bi tsagerun har cikin daji, an gano su yayin da suke raba kudin fansan da suka karba daga iyalan wadanda suka sacen.
Ya kuma bayyana cewa, tsagerun sun bude yayin da suka ga 'yan sanda na yin kansu.
A cewarsa, bayan musayar wuta an jikkata 'yan fashi biyu kuma an zarce dasu asibitin horarwa na jami'ar Ilorin.
Rahoton da muka samo daga jaridar ya ce daga baya an tabbatar da mutuwar tsagerun a asibitin.
Ya kara da cewa:
"Saboda haka, an tattara gawarwakinsu zuwa dakin ajiyar gawa na asibitin domin yin musu binciken gawa.
Abubuwan da aka kwato daga hannun tsagerun
Ya kuma ce, an kwato wasu kayayyaki daga hannun 'yan ta'adda da suka hada da; mota kirar Honda Accord Saloon mai lamba, LAGOS GJ 52 LSR, bindiga daya da kuma kudi da ba a bayyana adadinsu ba.
Ya ce akwai tsagerun da suka tsere, kuma rundunar na aiki tukuru don tabbatar da kamo su da gurfanar dasu, rahoton The Guardian.
Mista Ajayi kuma ya tabbatar da cewa wadanda aka ceton tuni sun sake saduwa da iyalansu.
A wani labarin, rahoton da muke samu ya ce, wata mata mai juna biyu da aka sace a Mando ta jihar Kaduna a watan Yulin da ya gabata ta haifi jariri a hannun 'yan bindiga, Daily Trust ta ruwaito.
Matar da aka sacen an ce ta je gaida mahaifiyarta da ke kwance bata da lafiya, an kuma yi awon gaba da ita ne da wasu kannenta mata biyu.
Asali: Legit.ng