Sana'a Sa'a: Mai Siyar Da Ayaba Ya Girgiza Intanet Yayin da Ya Yi Shiga Kamar Mai Zuwa Ofis

Sana'a Sa'a: Mai Siyar Da Ayaba Ya Girgiza Intanet Yayin da Ya Yi Shiga Kamar Mai Zuwa Ofis

  • An gano wani mutum da ke kasuwancinsa cikin salo yana siyar da gasasshen ayaba a bakin hanya
  • Mutumin mai suna Patrick Fosu ya yi fice saboda yanayin shigar da yake yi zuwa wajen sana’arsa kamar mai zuwa ofis
  • Sai dai kuma ya yi korafi kan tozarcin da yake fuskanta daga hukumomin gwamnati wadanda ke gizga shi a kullun saboda wajen da yake zama

Accra, Ghana - Patrick Fosu, wani mutumin kasar Ghana da ke siyar da gasasshen ayaba ya yi fice saboda yanayin yadda yake shiga zuwa wajen sana’arsa.

Fosu na shigar zanzaro kamar mai zuwa ofis a duk lokacin da zai je wajen sana’arsa wanda yake yi a bakin hanya a Accra.

Mai gasa ayaba
Sana'a Sa'a: Mai Siyar Da Ayaba Ya Girgiza Intanet Yayin da Ya Yi Shiga Kamar Mai Zuwa Ofis Hoto: LinkedIn/Andy Dankyi Oppong and Mabelin Santos/Getty
Asali: UGC

Hotunan Fosu wanda Andy Danky Oppong ya wallafa a shafin Linked ya ja hankalin mutane da dama a kan intanet.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

A cikin hotunan, an gano Fosu sanya da farar riga wanda ya ci zanzaro da kuma igiyan wuya wanda ya dace da shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majalisar Babban Birnin Accra ta kore ni daga tashar Spanner

Sai dai kuma, Mista Fosu ya yi korafi cewa hukumomin gwamnati na yawan damunsa saboda wajen da yake tsayawa yin kasuwancinsa.

Ya ce:

“Majalisar Babban Birnin Accra ta kore ni sau da dama daga wannan waje, amma sai na kara risker kaina a nan.
“Jami’an A.M.A ne ke damun mu a nan, sun zuwa sai su koremu daga nan.”

A cewarsa, hukumomin sun taba tura shi gidan kurkuku bayan sun gano shi a wajen kuma yak i ya bar wajen wanda ya bayyana a matsayin matattarar ciniki. Amma sai wani alkali ya sake shi.

Abun Ba Sauki: Matashiyar Baturiya Da Aka Gano Tana Tallan Gyada Ta Magantu A Sabon Bidiyo

Kara karanta wannan

‘Dan takara Ya Ba Gwamnati Satar Amsar Magance Matsalar ASUU a Kwana 30

A wani labarin, mun ji cewa bayan ta karade titin Lagas tana tallan gyada, matashiyar baturiya mai suna Pia, ta siye zukatan yan Najeriya da dama.

Ta wallafa sabon bidiyo inda take bayanin yadda harkoki suka gudana a wannan rana da kuma dalilinta na aikata abun da ta yi.

A cewar Pia, ta so yin hulda da mutane ne da kuma jin abun da ake ji a cikin talla a karkashin rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng