Harin 9/11 Na Amurka: Fasto Adebayo Ya Bayyana Yadda Aka Bincike Shi Saboda Yunkurin Siyan Jirgi
- Fasto Enoch Adeboye ya bayyana yadda ya kusa shiga matsala da hukumomin kasar Amurka shekaru da dama da suka shige
- Shugaban na cocin RCCG ya ce hukumomin Amurka sun gudanar da bincike kan siyan jiragen sama a kasar bayan harin kunar bakin wake da aka kai kasar
- Ya ce wasu manyan biloniya hudu sun yi yunkurin siya masa jirgin sama amma ya ki amincewa
Fasto Enoch Adeboye na cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) ya bayyana yadda ta kusa cikawa da shi a harin bam da wasu yan ta’adda suka kai kasar Amurka a shekarun baya.
Adeboya ya ce lamarin ya faru ne lokacin da hukumomin Amurka suka fara gudanar da bincike kan wadanda ke da hannu a harin.
Babban limamin na cocin RCCG ya ce abun ya samo asali ne lokacin da wasu manyan biloniya hudu suka yi yunkurin siya masa jirgin sama nasa na kansa amma sai ya ki.
A daya cikin wa’azinsa, malamin addinin ya ce lamarin ya faru ne shekaru da dama da suka wuce lokacin da naira ke da daraja sosai don har ta fi dala daraja, PM News ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce har mutanen sun tuntubi daya daga cikin ‘ya’yansa wanda ke aiki a kamfanin jirgin sama na Amurka a kasar Amurka.
Yace dole ya dakatar da su domin siyan jirgi wani abu ne, kula da lafiyar jirgin kuma wani abu ne mai zaman kansa. Ya ce masu shi kudi yake so da zai cina cocina.
Jaridar ta nakalto Adeboye yana cewa:
“A wani mataki a tarihin RCCG, wasu mambobi a nan sun hadu sannan suka yanke shawarar za su siya mun jirgin sama. Ina maganar shekaru da dama da suka shige;bay au ba. Sai da na dakatar da su saboda na ji labarin shirinsu. Sun rigada sun tuntubi daya daga cikin yarana da ke aiki da kamfanin jirgin sama na Amurka a Amurka
“Ta yaya za mu samawa fastonmu jirgin sama da aka yi amfani da shi main kyau?” sai da na dakatar da su; nace “Ah! Siyan jirgin sama abu guda ne; kula da shi kuma wani abun ne. cewa yanzu haka, ina bukatar kudin gina cocina, ba jirgin sama ba.”
“Koda baku yarda dani ba, toh, akwai shaida. Da harin 9/11 ya afku, sannan Amurka na kokarin gano da wa da wanene ke kokarin tayar masu da bam, sun ga wani rikodin murya. Kun san duk wani kira da ka yi zuwa Amurka ana nadansa.
“Idan baku sani ba, ku sani yanzu. Sun gani a bayanansu cewa akwai wasu mutane a Najeria da ke kokarin siyan jirgin sama daga kamfanin jirage na Amurka. Don haka sai suka tura jami’ansu don su dauko dana a chan.
“Don gano abun da ya faru kan wannan abu. Sai suka gano cewa fasto aka so siyawa jirgin. Sannan suka ga cewa fasto ba zai zama dan kunar bakin wake ba. Wannan ne kai!”
2023: Dogara Da Babachir Sun Gana Da Kiristocin Arewa Don Kalubantar Gamin Tinubu Da Shettima
A wani labari na daban, manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Hon. Yakubu Dogara da Babachir David Lawal, suna ci gaba da nuna rashin gamsuwarsu a kan tikitin Musulmi da Musulmi, cewa za su ci gaba da fafutuka don ganin an yi adalci.
Dogara, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai, shine ya bayyana hakan bayan ganawarsu da shugabannin kiristoci daga jihohin arewa 19 da babbar birnin tarayya a ranar Talata.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya kasance Musulmi shine dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023, inda jam’iyyar ta sake zakulo tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima wanda shima Musulmi ne don ya zama abokin takararsa.
Asali: Legit.ng