Gwamnatin Najeriya Za Ta Kawar da Amfani da Kananzir Nan da Shekarar 2023

Gwamnatin Najeriya Za Ta Kawar da Amfani da Kananzir Nan da Shekarar 2023

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce nan ba da jimawa ba zai tabbatar da an daina amfani da kananzir a Najeriya
  • Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taro da aka yi, ministar kudi ce ta wakilce shi
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da kuka kan yadda farashin iskar gas ke kara kamari a Najeriya tun hawan Buhari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Domin magancewa da samar da mafita ga matsalolin da suka shafi sauyin yanayi, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar haramta amfani kananzir nan da shekarar 2030, The Nation ta ruwaito.

Hakazalika, ta kuwa yanke shawarar kawar da gurbatattun kayayyaki a fannin man fetur da iskar gas nan da shekarar ta 2030.

Wannan na fitowa ne daga shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja, a wajen bude taron hada-hadar kudi karo na 15 da cibiyar ‘Chartered Institute of Bankers of Nigeria (CIBN) ta shirya.

Kara karanta wannan

Atiku ya sha alwashin yin abin da Buhari ya gaza idan aka zabe shi a 2023

Buhari ya ce a kawo karshen amfani da kananzir a Najeriya
Gwamnatin Najeriya za ta haramta amfani da kananzir nan da shekarar 2023 | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Buhari ya samu wakilcin ministar kudi ta Najeriya, Zainab Ahmed a taron, inda ta yi bayanin kadan daga illar hayaki ga yanayi a duniya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Domin a magance wannan matsala, gwamnati ta tsara yadda za ta rage yawan fitar hayaki a Najeriya."

Ta kuma yi nuni da cewa, gwamnati za ta ci gaba da dakile matsalolin hauhawar farashin kayayyaki ta hanyar shirye-shiryenta na tallafawa jama’a, rahoton Vanguard.

Ta kuma shaida cewa, a kasa mai tasowa kamar Najeiya, matsalar hauhawar farashin kayayyaki na kara ta'azzara da durkusar masu karamin karfi.

Karshe ta danganta hauhawar farashin kayayyaki a duniya da karuwar bukatun jama'a tun bayan barkewar annobar Korona a 2020 da kuma a baya-bayan nan tashin yakin Rasha da Ukraine.

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

Kara karanta wannan

'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

A wani labarin, jaridar Punch ta ruwatio cewa, masana sun gargadi 'yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za su fara siyan iskar gas a kan farashi mai tsananin tsada.

Wannan kenan a cewar 'Yan kasuwa na Iskar Gas. 'Yan kasuwar sun nuna damuwar su kan karancin shigo da gas da ke haifar da hauhawar farashinsa.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, 'yan kasuwan sun yi gargadin cewa iskar gas mai nauyin kilo 12.5 da a halin yanzu ake sayar dashi sakanin N7,500 zuwa N8,000 na iya tashi zuwa N10,000 kafin watan Disamba idan ba a yi wani abu don magance tsadar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.