'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana 'yan Boko Haram da 'yan damfara kuma masu zamba a kasar nan
  • Ya kara da bayyana cewa mulkinsa yayi matukar kokari sai dai wadanda ya dace su yaba masa sun tsuke bakunansu
  • Buhari ya bayyana yadda ya kwato wasu sassan arewa maso gabas daga hannun 'yan ta'adda kuma ya yabawa Gwamna Zulum kan kokarinsa

Imo - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bayyana ‘yan ta’addan Boko Haram a matsayin ‘yan damfara da gwamnatinsa ta durkusar tun a shekarar 2015.

Channels TV ta rahoto cewa, Buhari ya yi wannan batu ne a Owerri, babban birnin jihar Imo yayin da Gwamna Hope Uzodimma ya karba bakunsa bayan ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin ta yi.

Baba Buhari
'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban ya zargi jiga-jigan kasar nan da rashin dubawa Najeriya, inda ya kara da cewa duk da cewa gwamnatinsa ta yi matukar aiki tukuru, wadanda ya kamata su yaba wa nasarorin gwamnatinsa sun ki yin magana.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Dira Jihar Imo Don Kaddamar Da Wasu Manyan Ayyuka

Ya kara da cewa duk da samun makudan kudi daga danyen man fetur, magabatansa sun kasa bunkasa ababen more rayuwa a kasar na.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bari in fada muku gaskiya, na dora laifin rashin dubawa kasar nan a kan manyan kasa.
“Tsakanin 1999 zuwa 2015 da muka karba mulki, zan so mutane su duba babban bankin kasa da kuma NNPC, abin da aka samu ya kai biliyan 2.1 bpd. Najeriya tana samun kudin shiga sau miliyan 2.1 a wannan lokaci amma duba yadda ababen more rayuwa, dubi hanyar, dubi layin dogo, an kashesu a takaice. Wutar lantarki har yau muna fama.
“Amma lokacin da muka zo, abin takaici, an saki mayakan, abin ya ragu zuwa rabin miliyan bpd. Har ila yau, abin takaici, farashin man fetur ya ragu daga $28 zuwa $37.”

- Buhari yace.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

Ya ci gaba da cewa kafin ya hau mulki a watan Mayun 2015 ‘yan ta’addan Boko Haram ne ke rike da wasu kananan hukumomi a jihar Borno amma hakan ya zama tarihi bayan ya karba mulki.

“Ku dubi matsalar Arewa-maso-Gabas, ku duba Borno ko Adamawa, kananan hukumomi nawa ne ke hannun gwamnati, nawa kuma ke hannun Boko Haram? ’Yan damfara, ko su waye, masu zamba ne! Amma yanzu kaje ka tambayi Gwamnan Jihar Borno mai kokari, Gwamna mai kokari. Gwamnatin Tarayya ce ke kan mulki a yanzu.
“A fannin lokaci da albarkatu, wannan gwamnati ta yi aiki nagari. Dole ne in ce saboda wadanda ya kamata su ce ba su fada ba. Ban san dalili ba."

- Cewar shugaban kasan.

An shafe kimanin shekaru 13 ana artabu da 'yan Boko Haram a Najeriya. Maharan sun yi awon gaba da daruruwan yara ‘yan makaranta da wasu marasa galihu.

An kuma tafka asarar rayuka a hare-haren bama-bamai da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ta dinga shiryawa.

Kara karanta wannan

Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng