Budurwa Ta Fito Fili, Ta Sha Alwashin Bai wa Diyar Ekweremadu Kodarta
- Wata budurwa mai suna Annastasia Michael ta bayyana cewa zata bai wa diyar Sanata Ekweremadu kyautar koda
- Ta sanar da cewa shekarunta 24 a duniya kuma bata shan giya, wanda tana da tabbacin kodarta tana da lafiya
- A cewar Michael, bata bukatar ko sisin kwabo saboda tana son tabbatar da cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne
Budurwa mai shekaru 24 mai suna Annastasia Michael, ta rubuta budaddiyar wasika ga diyar Sanata Ike Ekweremadu, Sonia, inda tace zata bata daya daga cikin kodojinta biyu domin ceto rayuwarta.
Wannan na zuwa ne bayan budurwa Sonia Ekweremadu mai shekaru 25 ta roki jama'a da su taimaka mata wurin bata kyautar koda don ceto rayuwarta, Punch ta rahoto.
A yayin martani ga rokon da tayi a Facebook ranar Litinin, Annastasia tace ta shirya bata daya daga cikin kodojinta idan dukkan 'yan uwanta sun gaza bata, ta kara da cewa tayi hakan ne domin nuna cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne.
Annastasia ta kara da cewa zata bata kodarta kyauta inda tayi addu'ar kodarta ta kasance daidai da ta Sonia.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa tuni ta aike da sako ta yanar gizo ga Sonia domin hakan.
Cikakken bayaninta:
Kyautar koda ga Sonia Ekweremadu.
"Ni Annastasia Michael Olamma ina son sadaukar da kodata ga Sonia Ekweremadu domin ceton rayuwarta. Na sa kaina zan yi hakan domin tabbatar da cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne.
"Idan wani daga cikin 'yan uwanta daga uwa, uba ko abokan haihuwa, ba zasu iya ceton 'yar uwarsu ba, ni zan iya bada nawa domin ceton Sonia kuma bana bukatar komai. Ina fatan tawa ta dace da tata.
"Shekaruna 24 kuma bana shan gida, don haka nake kyautata zaton kodata tana da lafiya.
"Na aike da sako ga adireshin email kamar haka @helpsonialive@gmail.com kuma ina jiran martaninta."
Diyar Sanata Ekweremadu Ta Roki Al’ummar Annabi Su Taimaka Mata Da Koda
A wani labari na daban, Sonia, diyar sanata Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, ta roki jama’a da su taimaka mata da gudunmawar koda.
Diyar dan majalisar ta yi wannan rokon ne a daidai lokacin da iyayenta suka shiga tsaka mai wuya a kokarinsu na ceto rayuwarta.
Asali: Legit.ng