Mutane Sun Jikkata, Shaguna Sun Kone Kurmus Yayin da Tukunyar Gas Ta Fashe a Jigawa
- Mutane da dama sun ji raunuka, shaguna da gidaje sun ƙone yayin da wata Tukunyar Gas ta fashe a jihar Jigawa
- Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar, Adamu Shehu, yace lamarin ya faru jiya Litinin da daddare a ƙaramar hukumar Babura
- Har yanzun babu wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon fashewar yayin da wasu ke kwance a Asibiti, inji kakakin NSCDC
Jigawa - An tattaro cewa mutane da dama sun ji raunuka daban-daban yayin da Gidajen mutane da Shaguna suka ƙone biyo bayan fashewar wata Tukunyar Gas a ƙaramar hukumar Babura, jihar Jigawa.
Kakakin rundunar tsaron Sibil Defence (NSCDC) reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Talata.
Yace lamarin ya faru ne lokacin da wata babbar Motar dakon kaya maƙare da Tukunyar Gas ta yi bindiga a Babura, kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto.
Kakakin NSCDC yace Gidaje da yawa da shagunan al'umma sun ƙone sakamakon faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa mutane da dama sun jikkata, amma har yanzu ba bu wanda ya mutu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Mummunan lamarin ya auku ne jiya da daddare, ranar Litinin 12 ga watan Satumba, 2022 da misalin ƙarfe 9:00 na dare," Inji shi.
Wane mataki mahukunta suka ɗauka?
Adamu Shehu ya bayyana cewa tuni aka garzawa da mutanen da suka jikkata babban Asibitin Babura domin ba su kulawar lafiya ta musamman, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A jawabinsa yace, "An tura jami'an kwana-kwana daga ƙaramar hukumar Haɗejia zuwa yankin domin su shawo kan wutar da ta tashi."
Bugu da ƙari, mai magana da yuwun NSCDC a Jigawa yace har yanzun babu cikakken bayani kan makasudin abinda ya jawo fashewar, a cewarsa duk abinda bincike ya gano za'a sanarwa al'umma.
A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Yayan Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Filato
'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun yi awon gaba da babban yayan ɗan takarar PDP da ya nemi tikitin gwamna a jihar Filato.
Mazauna yankin sun tabbatar da faruwar harin ranar Asabar, sun ce maharan sun nemi a tattara musu miliyan N100m na fansa.
Asali: Legit.ng