Dakarun Sojin Najeriya Sun Ceto Mutum 6 da Aka Yi Garkuwa dasu a Kaduna

Dakarun Sojin Najeriya Sun Ceto Mutum 6 da Aka Yi Garkuwa dasu a Kaduna

  • Rundunar sojin Najeriya ta ceto wasu mutum shida da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kangon Kadi dake Chikun
  • Wannan na zuwa ne kasa da sa'o'i 48 bayan da sojojin suka halaka 'yan bindiga da suka kai farmaki NDA da FCE a Kaduna
  • An ceto mutane shidan ne bayan 'yan bindigan sun hangi sojoji sannan suka arce tare da barin wadanda suka yi garkuwa da su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Kasa da sa'o'i 48 bayan halaka wadanda suka shirya karantsayen tsaro a Makarantar Horar da Hafsoshin Soji ta Kaduna da satar daliban kwalejin gandun daji, dakarun sojin Najeriya sun ceto wasu mutum shida a yankin Kangon Kadi dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Taswirar Kaduna
Dakarun Sojin Najeriya Sun Ceto Mutum 6 da Aka Yi Garkuwa dasu a Kaduna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar ranar Litinin, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a APC yayin da mambobi 5,000 suka sauya sheka zuwa PDP a jihar Arewa

Aruwan yace kamar yadda dakarun suka bayyana karkashin Operation Forest Sanity, sun je aikin kakkabe daji daga Damba zuwa Kangon Kadi kuma tarar da wurin wasu 'yan bindiga a kusa da Kangon Kadi, Labi da kogin Udawa, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kamar yadda yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yan bindiga sun tsere daga yankin Kangon Kadi sakamakon ruwan wuta da dakarun suka sakar musu inda suka bar mutum shida da suka yi garkuwa da su.
"Wadanda aka ceto sun hada da Iliya Gide, Rabi Ali, Hussaina Gide, Naomi Nuhu da diyarta Pamela Barage.
"Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya amshi rahoton tare da godiya inda ya yabawa dakarun kan yadda suka dage wurin ganin karshen ta'addanci.
"Za a bayyana wa jama'a duk wani cigaba da ake samu."

Hotuna: Dakarun Soji Sun Kai Harin Kwantan Bauna, Sun Halaka 'Yan Boko Haram 7 a Borno

Kara karanta wannan

Hotuna: Dakarun Soji Sun Kai Harin Kwantan Bauna, Sun Halaka 'Yan Boko Haram 7 a Borno

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadin Kai, OPHK, sun kai harin kwantan bauna kan 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Zakakuran sojin Najeriyan sun kai harin ne a yankin Kasuwan Daula dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Wani jami'in sirri ya sanar da Zagazola Malama, kwararre wurin yaki da ta'addanci kuma mai kiyasi a fannin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa dakarun sun samu wannan nasarar ne bayan sun samu bayanan sirri kan cewa 'yan ta'addan suna dawowa daga kasuwa bayan sun yi wasu harkokin kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng