Yadda Gwamnatin Jihar Kogi Ta Gudanar Da Jana'izar Mutane 130 Da Babu Masu Shi

Yadda Gwamnatin Jihar Kogi Ta Gudanar Da Jana'izar Mutane 130 Da Babu Masu Shi

  • Gwamnatin Kogi ta gudanar da jana'izar gawarwaki 130 da masu shi basu fito da nuna nasu bane
  • Mamatan sun hada da mutanen da hatsarin mota, fashi da makami da garkuwa da mutane ya ritsa da su
  • Hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar ta ce kimanin watanni bakwai kenan da aka ajiye gawarwakin a FMC Lokoja don haka ya zama dole a binne saboda tsaron muhalli

Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta binne gawarwaki guda 130 da aka rasa masu shi wadanda aka ajiye a cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Lokoja.

An tattaro cewa gawarwakin sun shafe tsawon watanni bakwai a FMC Lokoja ba tare da iyali ko yan uwansu sun fito sun ce nasu bane.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Shiga Zullumi Bayan An Gano Gawar Dalibai Mata 3 Na Jami'ar Najeriya A Dakin Kwanansu

An binne su ne a wata makabarta da ke yankin Falele-Lokoja, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jahar Kogi
Babu Masu Shi: Gwamnatin Jihar Kogi Ta Binne Gawawarwaki 130 Hoto: Punch
Asali: UGC

Mamatan sun kasance mutanen da hatsarurruka ya ritsa da su, wadanda fashi da makami da kuma garkuwa da mutane ya cika da su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugabar Hukumar Kula da tsaftar muhalli da shara ta Jihar Kogi, Misis Arokoyo Elizabeth, wacce ta bayyana hakan, ta ce hukumar ta samu goyon bayan doka don tabbatar da tsaron muhalli.

Elizabeth wacce ta samu wakilcin mukaddashin sakataren hukumar, Ajayi Olufemi, ta ce jami’an yan sanda da na hukumar kula da hana afkuwar hatsarurruka (FRSC) ne suka kai gawarwakin dakin ajiye gawa.

Ta ce sanarwar da ake ta yi a kafofin watsa labarai cewa iyalai da dangin da basu ga wani nasu ba su zo don duba gawarwakin ya ci tura.

Jaridar Punch ta nakalto ta tana cewa:

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

“Muna ta bayar da sanarwa a gidajen radiyo, talbijin da sauran kafofin watsa labarai game da wadannan gawarwaki. Amma, har zuwa yanzu da nake maku magana, ba a ji komai daga bangaren iyalai, yan uwa da abokan mamatan ba.
“Don haka, dole a binne su saboda sun dade a dakin ajiye gawa ba tare da an zo daukarsu ba.”

Sakamakon Binciken da Muka Gudanar Kan Tukur Mamu Yana Da Daure Kai, DSS

A wani labari na daban, hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce sakamakon binciken da ta gudanar kan Tukur Mamu akwai ban mamaki sosai, Daily Trust ta rahoto.

Da take martani ga furucin da shahararren malamin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi yayi, hukumar ta ce ba za ta bari ta shagaltu ba.

Gumi ya zargi DSS da aikata ta’addanci, yana mai kalubalantar rundunar yan sandan ta farin kaya da ta saki Mamu, wanda ya kasance hadiminsa ko kuma ta gaggauta gurfanar da shi a kotu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta gindaya wasu sharruda ga gidajen rediyo kan wakar Ado Gwanja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng