Ni Ba Yarinya Bace: Wata Budurwa 'Yar Tsurut Ta Fashe Da Kuka Bisa Yadda Wasu Ke Mata Kallon Yarinya

Ni Ba Yarinya Bace: Wata Budurwa 'Yar Tsurut Ta Fashe Da Kuka Bisa Yadda Wasu Ke Mata Kallon Yarinya

  • Wata budurwa yar tsurut ta yiwa jama’a da mabiyanta karin haske kai tsaye cewa ita din babba ce ba yarinya ba
  • Mutane na yiwa budurwar mai yar karamar murya da fuskar yara kallon karamar yarinya saboda yanayin halittar da Allah ya yi mata
  • A cewar matashiyar wacce ke cike da kwarin gwiwa, tana fama da wani nau’in rashin lafiya da ke hana mutum girma ne wanda shine dalilin kasancewarta yar tsurut

Wata matashiya mai karamin jiki da ke nishadantar da mutane a dandalin TikTok ta bayyana cewa ita din ba karamar yarinya bace domin ta balaga.

Matashiyar mai suna @itzamealiaa a TikTok tana da karamin jiki da kuma siriryar murna irin ta kananan yara kuma hakan yasa mutane da dama yanke hukuncin cewa ita din yarinya ce kankanuwa.

Budurwa
Ni Ba Yarinya Bace: Wata Budurwa 'Yar Tsurut Ta Fashe Da Kuka Bisa Yadda Wasu Ke Mata Kallon Yarinya Hoto: TikTok/@itzamealiaa
Asali: UGC

A wani bidiyo da ta yada a dandalin, budurwar wacce ke cike da karfin gwiwa ta bayyana cewa tana fama da wani nau’in cuta ne da ke kankantar da mutun wanda shine dalilin kasancewarta yar tsurut.

Kara karanta wannan

Matashiyar Budurwar Najeriya Ta Wanke Kafa Har Turai Don Ganawa Da Baturen Da Ta Hadu Da Shi A Yanar Gizo

Kamar yadda shafin Rare Diseases ya bayyana, cutar RSS yana sanya yara kin girma bayan haihuwarsu sannan sukan kasance da katon kai, katan goshi, karamin fuska da rashin son cin abinci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matashiyar ta kuma bayyana cewa shekarunta 22 a duniya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

The Open Book ya ce:

“Muryarta da karfinta ne suka birgeni sai da na murmusa…”

GAB ta vce:

“Bayani cike da kauna, kina da kyau a ciki da waje.”

Sexyred ta ce:

“Ba sai kin yi bayani ba yan mata ina da wata gajeriya a ajina kuma mutane ne masu ban mamaki.”

Matashiyar Budurwar Najeriya Ta Wanke Kafa Har Turai Don Ganawa Da Baturen Da Ta Hadu Da Shi A Yanar Gizo

A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya mai suna Kemisola ta hadu da baturen saurayinta da suka shafe tsawon watanni 6 suna soyayya ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ya Koma Jami'ar Da Yayi Karatu, Yace Su Bashi Kudinsa Su Karbi Kwalinsu

Budurwar wacce ta cika da farin ciki ta je dandalin TikTok don yada bidiyon haduwarsu ta farko da mutumin.

Ta dauki bidiyon yadda ta isa filin jirgin sama na Najeriya tare da wata kawarta sannan ta shiga cikin jirgi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel