Yajin-aiki: Rikakkun Farfesoshi da SANs 46 Za Su Kare ASUU a Kyauta a Gaban Kotu

Yajin-aiki: Rikakkun Farfesoshi da SANs 46 Za Su Kare ASUU a Kyauta a Gaban Kotu

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari tayi karar kungiyar ASUU a kotun kwadago domin a janye yajin-aiki
  • Malaman jami’a ba su da niyyar komawa aiki sai an biya masu bukatunsu, sun tanada tulin Lauyoyinsu
  • Farfesoshin jami’a da manyan Lauyoyi da sun kai matsayin SAN za su kare ASUU ba tare da an biya su ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - ‘Ya ‘yan kungiyar ASUU wadanda sun kware a harkar shari’a za su kare malaman jami’a a shari’ar da za ayi tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

Sun ta kawo rahoto cewa malaman jami’a da sun kai mataki da SAN a Najeriya da kuma Farfesoshin shari’a 46 ne za su zama lauyoyin kungiyar ASUU.

Punch tace wani daga cikin ‘yan majalisar koli na kungiyar ASUU yace za suyi amfani da lauyoyin da suke da su a jami’o’in gwamnatin kasar nan.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

Wannan malamin jami’a da bai bari an kama sunansa ba, yace ASUU tana da Farfesoshin shari’a da manyan Lauyoyi na SAN da za su tsaya mata.

Za a hadu a kotu a yau

“Shugaban kungiya za iyi wannan jawabi, amma za mu je kotu a yau (Litinin); muna da SAN da Farfesoshi a cikin ‘yan kungiyarmu, za su kare ASUU a kyauta.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Wani 'Dan majalisar NEC

Hakan na zuwa ne bayan an dakatar da biyan malaman makarantar albashi, an kuma kafa kwamitoci da nufin kawo karshen wannan dogon yajin-aiki.

Lauyoyi
Sababbin zama SAN a Najeriya Hoto: solacebase.com
Asali: UGC

Ku yi gum da bakinku - ASUU ga malamai

Wata majiyarmu ta shaida mana cewa shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya umarni malaman jami’a suyi tsit a kan maganar shari’ar.

Farfesa Osodeke ya yi alkawari kungiyar za ta maidawa gwamnati martani yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Bayyana Illar da Obi Zai Yi Masu, Ya Ayyana Magajin Buhari

Mataimakin shugaban ASUU na kasa, Dr. Chris Piwuna ya tabbatar da cewa za su hallara a kotu yau domin su kare kansu, yace sun shiryawa gwamnati.

Dr. Piwuna yake cewa gwawarmayar malaman jami’a ta gaji irin wannan kalubale a tarihi.

Da Punch ta zanta da shugaban ASUU na reshen jami’ar FUT Minna, Dr. Gbolahan Bolarin, yace sun shirya, duk da sun yi mamakin matakin da aka dauka.

An koma kotu

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi ya shigar da karar ASUU a madadin gwamnatin tarayya a gaban kotun kwadago na kasa da ke zama a Abuja.

Gwamnati ta je kotu saboda malaman jami’ar sun rufe makarantu, sun tafi yajin-aiki tun Fubrairu. An yi watanni ana kokarin a sasanta amma abin ya gagara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng