Sheikh Ahmad Gumi Yayi Maganarsa Ta Farko Kan Kama Tukur Mamu

Sheikh Ahmad Gumi Yayi Maganarsa Ta Farko Kan Kama Tukur Mamu

  • Sheikh Ahmad Gumi ya yi tsokacinsa na farko kan lamarin damke Tukur Mamu a jihar Kaduna
  • Babban Malamin ya kasance kokarin sulhun gwamnati da yan bindiga masu garkuwa da mutane
  • Hukumar DSS ta kama Tukur Mamu a kasar Misra yana hanyar tafiya kasar Saudiyaa ibadar Umrah

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Shahrarren Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga Hukumar tsarin farin kaya, DSS, ta gaggauta sakin Tukur Mamu ko ta kai shi kotu.

Gumi ya bayyanawa gwamnati cewa dokar kasa bata amince a rike mutum sama da kwana guda ba'a kai shi kotu ba.

A zaman karatun littafin Muktasarul-Khalil da Malamin ke yi mako-mako a Masallacin Sultan Bello dake Kaduna, Gumi yace wannan jarabawa ce ga Tukur Mamu kuma Allah ya sa yaci jarabawar.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

Sheukh Gumi
Sheikh Ahmad Gumi Yayi Maganarsa Ta Farko Kan Kama Tukur Mamu Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

A bidiyon karatun da Malam ya daura a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Na san sharrin Security (jami'an tsaro), domin (shin) Sardauna ya tsira daga sharrin Security (jami'an tsaro), Murtala ya tsira daga sharrin Security (jami'an tsaro), Maimalari ya tsira daga sharrin Security (jami'an tsaro), IBB ya tsira daga sharrrin Security, shi kanshi Buharin ya tsira daga sharrin Security (jami'an tsaro)?."
"Ni na san abinda ku baku sani ba. Ni shawara nike bawa hukuma ta sakeshi a mance da lamarin mu roke shi yayi hakuri."
"Muna kira ga hukumar tayi mishi adalci, kundin tsarin mulkin kasa yace kada ka kama mutum sai ka samu hujja wanda gobe-gobe zaka kaishi kotu, kuma in kun samu hujja mara karfi sosai ku kai kotu sai kotu tace a cigaba da rikeshi, shine doka.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 da ya Dace a Sani Game Da Tukur Mamu, Hadimin Gumi da DSS Suka Kama

"Muna yaki da yan ta'adda saboda basa bin doka, Idan gwamnati bata bin doka kuma tana rike da makami itama ta zama yar ta'adda, me banbancinsu?"

Kalli bidiyon:

An Damke Tukur Mamu A Kasar Misra Bisa Umurnin Gwamnatin Tarayya

Jami'an tsaron birnin Kahira a kasar Masar sun damke mai kokarin sulhu tsakanin yan bindiga da iyalan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna tare da iyalansa.

Tukur Mamu na hanyarsa ta tafiya kasar Saudiyya gudanar da Ibadar Umrah yayinda aka tsareshi a tashar jirgin Kahira na kwana guda.

Dirarsa jihar Kano ke da wuya, jami'an DSS suka same damkeshi kuma suka garzaya da shi ofishinsu.

Daga baya suka shiga gidansa da ofishinsa dake Kaduna suka shiga lalube. Sun yi ikirarin cewa sun samu kudade da kayan Sojoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel