Shugabannin Kiristoci Sun Shirya Zama Da Dukkan Yan Takara Kujeran Shugaban Kasa

Shugabannin Kiristoci Sun Shirya Zama Da Dukkan Yan Takara Kujeran Shugaban Kasa

  • Gamayyar shugabannin Kirista ta shirya zaman gabatar da bukatar Kiristoci da yan takaran kujeran shugaban kasa
  • Shugabannin sunce Musulmai tuni sun yi tsarin yadda zasuyi kane-kane kan mulki amma Kiristoci sun gafalta
  • Shugabar taron tace duk dan takaran da yaki zama da su ya shirya shan kaye a zaben 2023

Abuja - Gabanin zaben 2023, gamayyar shugabannin kiristocin Najeriya tace tana shirya zama da duk dan takarar kujeran shugaban kasan dake son cin zabe, rahoton Punch.

Gamayyar ta Nigerian National Christian Coalition ta bayyana cewa duk dan takaran da yaki zama da shugabannin Kirista ba zai ci zabe ba.

Kodineta shirya taron, Titi Oluwadare, ta bayyana cewa:

"A zaben 2023, wajibi ne ya zauna da Kiristoci, ko ka fadi zabe. Dole shugabanni su sani rayuwa da zaman lafiya na da muhimmanci."

Kara karanta wannan

Katsina: Yadda Yarinya Mai Shekaru 13 Ta Haddace Qur'ani, Ta Rubuta shi da Hannunta

Ana shirya zaman ne tsakanin shugabannin Coci da yan siyasa domin gabatar musu da bukatun mabiya addinin Kirista don sanin wanda zai yi da su, cewarta Titi.

An shirya zaman ranar 20 ga Satumba, 2022 a farfajiyar International Conference Centre, dake birnin tarayya Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan Takara
Shugabannin Kiristoci Sun Shirya Zama Da Dukkan Yan Takara Kujeran Shugaban Kasa
Asali: Facebook

A cewarta, Kiristoci sun gaji da zuba ido a siyasar kasar nan kuma duk dan takarar da ya ki yi da su zai sha kasa a 2023.

Oluwadare tace tikitin Musulmi-Musulmi da jam'iyyar All Progressives Congress APC tayi ya zama wajibi a dakatad da ita kafin kasar ta ruguje.

Ta kara da cewa Musulmai sun yi tsarin yadda zasuyi kane-kane kan mulki amma Kiristoci sun gafalta.

A jawabin da ta yiwa manema labarai ranar Juma'a, tace:

"Yanzu Coci ta farka daga barcinta kuma shirye muke mu tattauna da masu ruwa da tsaki. Ba zamu sake yarda a mayar da mu saniyar ware ba, ayi amfani da mu kuma ayi watsi da mu."

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti da Osun: INEC ta ce wasu madatsa sun farmaki tashar yanar gizonta

Har Abada Ba Zamu Yarda Da Takarar Musulmi da Musulmi Ba, Kungiyar CAN

Tuni Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta jaddada cewa bata sauya ra'ayi game da takarar Musulmi da Musulmi bayan zamanta da dan takarar shugaban APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

CAN tace a daina siyasantar da halartar Tinubu bikin cikar Fada Matthew Kukah shekaru 70 da akayi a Abuja kuma bata amsa kudi daga hannunsa ba.

Shugaban CAN, Daniel Okoh, ya bayyana hakan a jawabin da mai magana da yawunsa, Luminous Jannamike, ya fitar

Asali: Legit.ng

Online view pixel