Lakcaran Najeriya Ya Rasu A Cikin Motarsa Yayin Da Dalibai Ke Jiransa A Aji
- Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci wani lakcara mai suna Hassan Momoh a sume a cikin motarsa a Auchi, Jihar Edo
- Rahotanni da aka tattara sun ce malamin yana shirin zuwa aji ya koyar ne amma ya gaza fita daga motarsa ya shiga ajin
- Wani abokinsa ya wallafa rubutu a shafin Facebook yana alhinin rashin lakcaran ya kuma ce tuni an masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci
Edo - Wani mai amfani da Facebook, Momodu Bameyi, ya yi alhinin rashin abokinsa, wani lackara, wanda ya rasu a cikin motarsa.
Bameyi ya bayyana cewa marigayin lakcaran yana da aji da zai koyar ne kuma ya tuka motarsa zuwa makaranta amma ya rasu a cikin motar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An tattaro cewa daliban lakcaran sun jira shi a cikin aji amma ba su gan shi ba, hakan yasa suka tafi inda motarsa ya ke su duba ko me ke faruwa.
Sun isa wurin da motarsa ya ke don tambayan dalilin da yasa ya dade bai shigo ba sai suka tarar yana sume.
An kira jami'an tsaro nan take suka taimaka suka kai shi asibiti. Amma, abin bakin ciki, mutumin ya rasu a hanyar zuwa asibitin.
Da ya ke wallafa hoton marigayin a Facebook, Momodu ya ce:
"Aboki na ya tuka motarsa zuwa makaranta, ya yi taro a department, ya gana da dalibai masu yin seminar kuma zai shiga aji. Ya tuka motarsa zuwa aji amma ya gaza iya fitowa daga motar. Ya rasu a hanyar kai shi asibiti. An birne shi bisa koyarwar addinin musulunci. Allah ya jikansa Hassan Momoh. Kuma kana nan kana cika baki?"
Masu amfani da shafin intanet sun yi martani
Nana Aishat ta ce:
"Allah ya gafarta masa dukkan kurakurensa ya saka masa da aljanna firdausi Ameen."
Ramadan Abdul ya ce:
"Allah ya saka masa da aljanna, Allah ya jikan malamin lissafin mu wancen lokacin."
Buraimah Meriam ta ce:
"Mutuwa dole ne. Allah ya saka masa da aljanna firdausi. Aamiin. Allah ya jikan malaman Accouting din mu a makarantar sakandare ta Poly".
Musa Abudutu ya yi martani:
"Allah ya gafarta masa kura-kurensa ya saka masa da Aljanna Firdausi."
Usman Dauda ya ce:
"Ba a san lokacin mutuwa ba. Tabbas za ta zo kuma ba za a iya kauce mata ba. Ina addu'ar Allah ya saka masa da aljanna firdausi. Aamiin."
Asali: Legit.ng