Kananan Yara 3 Sun Mutu A Ginin Da Ya Rufta A Jigawar Tsada
- Wasu kananan yara guda uku sun rasu a kauyen Jigawar Tsada da ke Jihar Jigawa sakamakon gini da ya rufta musu
- Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Jigawa ta tabbatar da rasuwar yaran kuma ta bada sunayensu da shekarunsu
- A baya-bayan nan, yan sandan sun sanar da rasuwar wasu mata hudu da jinjiri daya a hadarin kwale-kwale a kauyin Guri a Jihar Jigawan
Jigawa - A kalla yara uku ne suka rasu a yayin da wani gini ya rufta a ranar Alhamis a karamar hukumar Dutse bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, in ji yan sanda, Premium Times ta rahoto.
Kakakin yan sandan Jigawa, Lawan Shiisu Adam, ya ce ginin ya rufta ne a Jigawar Tsada saboda ruwan sama wanda aka yi awanni ana yi a daren ranar Laraba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yan sandan sun ce wadanda suka rasun sune Farida Idris, 6, Mariya Idris, 3, da Bilkisu Yahya, mai shekara daya da watanni shida duk mazauna kauyen Yakasai a kauyen Jigawar Tsada a karamar hukumar Dutse.
Daily Trust ta rahoto yan sandan sun ce dukkan wadanda abin ya shafa sun mutu nan take kafin a ceto su.
Sanarwar da yan sandan suka fitar ta ce:
"Bayan samun rahoton, yan sandan sun isa wurin, suka kwashi wadanda abin ya faru da su zuwa babban asibitin Dutse.
"Da isarsu, likitan da ke bakin aiki ya tabbatar sun rasu. An dauki hotunan gawarsu sannan aka bawa yan uwansu don yi musu jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.
"Kwamishinan yan sandan Jigawa, Aliyu Tafida, ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa kuma ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu."
Jinjiri Dan Wata 7 Da Mata 4 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale A Jigawa
A wani rahoton, rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Jigawa ta tabbatar da rasuwar jinjiri dan wata bakwai da mata hudu a hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Guri.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar, DSP Lawan Shiisu, ne ya tabbatar da afkuwar lamarin a Dutse, ranar Laraba, rahoton Daily Trust.
Ya ce mutanen yankin sun yi kokari ceto fasinjojin, ya kara da cewa sun ciro gawarwakin su.
Asali: Legit.ng