Sojoji Sun Ragargaji Yan Ta'adda A Hanyar Kaduna Zuwa Zaria, Sun Aika Da Wasu Barzahu

Sojoji Sun Ragargaji Yan Ta'adda A Hanyar Kaduna Zuwa Zaria, Sun Aika Da Wasu Barzahu

  • Dakarun sojoji a Jihar Kaduna sun yi nasarar halaka yan ta'adda guda biyu a hanyar Kaduna zuwa Zaria a karamar hukumar Igabi
  • Mista Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar
  • Aruwan ya ce gwamnatin Jihar Kaduna ta yi murnar samun labarin ta kuma bukaci sojojin su kara kaimi wurin ganin kawo karshen bata garin

Jihar Kaduna - Dakarun sojojin Najeriya sun bindige wasu yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Zaria a karamar hukumar Igabi, Leadership ta rahoto.

Sojojin, bayan samun bayanan sirri, sun yi wa yan bindigan kauton bauna a wurin, suka kashe biyu daga cikinsu.

Sojojin Najeriya
Sojoji Sun Ragargaji Yan Ta'adda A Hanyar Kaduna Zuwa Zaria, Sun Aika Da Wasu Barzahu. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Mista Samuel Aruwan, kwamishinan a ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yakar talauci: Gwamna ya ba da umarnin a mayarwa mahajjata wani adadi na kudin da suka biyu na hajji

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da shigarsu wurin, sojojin suka fara yi wa yan bindigan ruwan harsashi yayin da yan bindigan suka yi kokarin mayar da martani. An kashe biyu daga cikin bata garin."

Gwamnatin Kaduna ta jinjina wa dakarun sojoji bisa kwazonsu - Aruwan

Aruwan ya ce gwamnatin jihar Kaduna ta yi farin cikin samun labarin ta kuma jinjinawa sojojin saboda amsa kirar cikin gaggawa.

Ya ce gwamnatin tana mika godiyarta ga dakarun sojojin da sauran jami'an tsaro yayin da ta ke karfafa musu gwiwa su cigaba da kokarin kawar da bata garin.

Aruwan ya yi kira ga al'umma su sanar da hukuma idan sun ga wani da raunin bindiga yana neman magani

Ya ce tunda mafi yawancin yan bindigan sun tsere da raunin bindiga, gwamnatin na kira ga mutane su kai rahoton duk wani wanda ba a yarda da shi ba da ke neman likita.

Kara karanta wannan

Mutum 43 Da Aka Sace A Masallacin A Zamfara Sun Samu Kubuta Bayan Biya Kudi, Daya Ya Mutu

Za a iya samun jamian tsaron a wadannan lambobin wayan 09034000060 da 08170189999, a cewar Aruwan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164