Sheikh Gumi Ya Magantu Kan Kamen Hadiminsa, Tukur Mamu, a Kasar Misra
- Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya tabbatar da cewa bai san dalilin kama hadimin, Tukur Mamu, ba
- Ya bayyana yadda ya ji labaran shima a kafafen yada labarai na yadda aka kama malamin da iyalansa a Cairo
- Ya sanar da cewa, gwamnatin Najeriya tun farko bata ayyana tana nemansa ba kuma bata bayyana wani zargi da take masa ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, yace basi da wani bayani kan dalilin da yasa aka damke hadiminsa, Malam Tukur Mamu a birnin Cairo, dake kasar Misra.
Kafafen yada labarai sun cika da ragotannin kama Mamu a kasar arewacin Afrika tare da iyalansa yayin da suka kan hanyarsu ta zuwa kasar Saudi Arabia domin yin Umra.
"Yanzu nake jin cewa an tsare shi a Cairo da iyalansa. Ban san dalilin faruwar hakan ba kuma har da saboda gwamnatin Najeriya bata zargesa da komai ba ko ta ayyana tana nemansa ba."
- Gumi yayi martani da People Gazette bayan sun tambayesa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Amma na ji cewa yana kan hanyar dawowa Najeriya, a don haka neka fatan samun karin bayani bayan isowarsa."
- Sheikh ya kara da cewa.
An kama Mamu tare da tsaresa a filin sauka da tashin jiragen sama na Cairo na sa'o'i 24 kuma an dawo da shi Najeriya kamar yadda Daily Trust ta bayyana.
"Ba a hantare ni ba a filin jirgi a Najeriya har sai da na kai Cairo lokacin da jami'an tsaro suka sanar min cewa an bada umarnin kama ni daga hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya.
"An kama ni da iyalaina na tsawon kwana daya a filin sauka da tashin jiragen sama na Cairo."
- Mamu ya sanar.
Jami'an DSS Sun Cafke Tukur Mamu a Filin Jirgin Kano
A wani labari na daban, jami’an tsaron farin kaya na DSS, sun kama Malam Tukur Mamu a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano.
Daily Trust ta rahoto yadda ‘yan sandan kasa da kasa suka kama Mamu a birnin Cairo dake Misra kuma aka dawo da shi gida Najeriya.
Tsohon mai sasancin tsakanin ‘yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja da iyalansu, yace yana kan hanyarsa ta zuwa Saudi Arabia ne yayin da aka kama shi tare da tsare shi na sa’o’I 24 a Misra.
Asali: Legit.ng