Da Duminsa: Buhari Ya Kafa Kwamitin Da Zai Duba Bukatun ASUU
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa sabon kwamitin da zai duba bukatun kungiyar malaman jami'o'i
- Kamar yadda Adamu Adamu, ministan ilimi ya bayyana, kwamitin ya kunshi iyayen jami'o'i 4 da shugabannin jami'o'i 4
- Ministan ilimi zai kasance shugaban kwamitin kuma za a duba bangaren kin biyan albashi da malaman ke yajin aiki da kuma karin albashi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin da zai duba bukatun kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU.
Kungiyar ta fada yajin aiki tun daga ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kan farfado da jami'o'in gwamnatin, alawus dinsu da kuma amfani da tsarin UTAS wurin biyan albashin malaman da sauransu.
Ana tsaka da yajin aikin, gwamnatin ta kallafa dokar babu biyan albashi inda tace ba za ta biya malaman albashi ba a cikin watannin da basu yi aiki ba, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malaman sun yi watsi da wannan hukuncin inda suka cigaba da yajin aikinsu.
Amma a taron da aka yi da shugabannin jami'o'in da kuma iyayen jami'o'in gwamnatin a ranar Talata a Abuja, Malam Adamu Adamu, ministan ilimi na kasar nan ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin sake duba lamarin.
Adamu yace kwamitin ya hada da iyayen jami'o'in hudu da shugabannin jami'o'in sannan da ministan matsayin shugaban kwamitin.
Yace kwamitin zai kara duba bukatun ASUU ballantana manyan bukatun da ba a duba ba kuma ba a samu matsaya ba.
Ministan yace zai labartawa Buhari yadda taron ya kasance. Yace kwamitin zai duba manyan wurare biyu da suka da rashin biyan albashi da kuma yawan albashin malaman jami'o'in.
Yayin da ba zai iya bada tabbataccen lokacin da kwamitin zai yi aiki ba, yace suna kallon kwanaki ne.
Yace suna kallon cewa sabon kwamitin zai dasa ne daga inda aka tsaya a kai sannan su samo maslaha.
Buhari ya Kara Alawus din Tafiye-tafiye: 250% na Manyan Sakatarorin Gwamnati, 128% na Ministoci
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince da karin alawus din yawon aiki, DTA, ga ministoci, manyan sakatarorin gwamnati da ma'aikatan gwamnati daga mataki na 1 zuwa 17.
Alawus din yawon aiki, DTA, yana nufin kudin da gwamnati a ke biyan ma'aikacin da yayi tafiyar aiki.
Asali: Legit.ng