Yanzu Yanzu: Allah Ya Yiwa Na Hannun Daman Kwankwaso, Kabir Magashi, Rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah Ya Yiwa Na Hannun Daman Kwankwaso, Kabir Magashi, Rasuwa

  • Tsohon dan takarar kujerar dan majalisar jiha mai wakiltan mazabar Gwale ta jihar Kano, Labaran Kabir Magashi, ya kwanta dama
  • Magashi wanda ya kasance na hannun daman dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya rasu a yau Talata
  • Hadimin Kwankwaso, Hassan Saifullahi ya tabbatar da rasuwar tsohon mamban na jam'iyyar PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Labaran Kabir Magashi, babban na hannun daman dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya rasu.

Magashi ya rasu ne a yau Talata, 6 ga watan Satumba kuma za a yi jana’izarsa a Unguwar Magashi.

Magashi da Kwankwaso
Yanzu Yanzu: Allah Ya Yiwa Na Hannun Daman Kwankwaso, Kabir Magashi, Rasuwa Hoto: Labaran Kabir
Asali: Facebook

Babu wani cikakken bayani game da mutuwar tasa, amma hadimin Kwankwaso, Hassan Saifullahi ya tabbatar da rasuwar tasa a shafinsa na Facebook.

Ya rubuta a shafin nasa:

Kara karanta wannan

Tsohon Hadimin Buhari Ya Shigo Takarar Gwamnan Kano Gadan-Gadan Daga Baya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Inalillahi Wa'inna'lahir raji'un.
“Allah ya yiwa Labaran Kabir Magashi Rasuwa yanzu. Allah ya jikansa da Rahama Ameen."

Marigayin ya kasance tsohon mamba na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), inda ya yi takarar kujerar dan majalisar jiha mai wakiltan mazabar Gwale ta jihar Kano, a zaben da ya gabata.

Zaman Lafiya A Kano: Ganduje Ya Fadi Babban Abin da Ya Sa Kano Ke Zaune Cikin Kwanciyar Hankali

A wani labari na daban, gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya danganta zaman lafiya da ake samu a jihar da mutuntawa da hakuri da ake yi tsakanin kabilu da addinai a jihar.

Ganduje ya kuma ce duk wasu kabilu da kungiyoyin addinai a kasar nan yan uwan juna ne, don haka akwai bukatar su rungumi zaman lafiya da hadin kai ba tare da la’akari da banbancinsu ba don samun ci gaba da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Hotuna: Kwankwaso Ya Ziyarci Jihar Benue, Ya Aiwatar Da Muhimmin Aiki

Gwamnan ya bayyana hakan ne a karshen mako a Kano yayin da yake jawabi a fadar sarkin Yarbawa na jihar, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel