Wawure N2.5bn: Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Belin Kakakin Majalisa Ogun
- Babbar Kotun tarayya dake zamanta a jihar Legas ta amince da bukatar Belin kakakin majalisar dokokin jihar Ogun
- Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'adi (EFCC) ta gurfanar da Olakunle Oluomo kan tuhumar karkatar da N2.5bn
- Yayin yanke hukunci kan bukatar Belin, Kotun ta kafa sharudda masu tsauri kan waɗan da ake tuhuma
Lagos - Babban Kotun tarayya dake zama a Legas ta ba da Belin kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Hon Olakunle Oluomo, kan miliyan N300m tare da mutum biyu da zasu tsaya masa.
Alƙalin Kotun, mai shari'a Daniel Osiagor, shi ne ya jagoranci bayar da Belin biyo bayan rashin taƙaddama daga hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin kasa ta'annadi (EFCC).
Channels TV ta ruwaito cewa tun farko an gurfanar da kakakin majalisar dokokin gaban Kotun ne kan zargin wawure kuɗi kimanin Biliyan biyu da rabi.
Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ya faɗa wa Kotun cewa zai bar batun Belin a hannun Kotu, ta yanke hukunci a iya hankalinta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A nashi ɓangaren kuma lauyan shugaban majalisa, Kehinde Ogunwumiju (SAN) ya roki mai shari'a ya bai wa wanda yake kare wa Beli.
Sharuɗɗan da Belin ya ƙunsa
Da yake amince wa da batun Belin, Mai shari'a Osiagor, ya yanke cewa wajibi ɗaya daga cikin mutanen da zasu tsaya wa wanda ake zargi, kada ya gaza kaiwa mataki na 16 a aikin gwamnati.
A cewar Alƙalin, ya zama tilas na biyun ya kasance ya mallaki kadarar fili a yankin da Kotun take zama.
Bayan haka, Babbar Kotun ta kuma amince da Belin waɗan da ake ƙara na biyu da na uku kan naira miliyan N100m da kuma mutum biyu da zasu tsaya musu da makamancin kuɗin.
'Bana Son Saɓa Wa Allah' Mata Ta Nemi Saki A Kotun Musulunci, Miji Yace Ta Biya Miliyan N1.6m Ya Saketa
Baki ɗaya waɗanda zasu tsaya wa mutanen da ake tafka shari'a a kansu, tilas su mallaki shaidar biyan harajin shekara sannan kuma su yi rantsuwa.
A wani labarin kuma Hukumar EFCC Ta Kama 'Yahoo Boys' 41 Da Dukiyoyin Da Suka Mallaka
Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo wanda aka fi sani da Yahoo Boys 41.
Matasan 'Yahoo Boy' sun shahara da sace kudaden mutane ta manhajojin bankin wayansu da kuma yanar gizo.
Asali: Legit.ng