Bana Son Saɓa Wa Allah, Mata Ta Nemi Saki A Kotun Musulunci, Miji Yace Ta Biya Kuɗi

Bana Son Saɓa Wa Allah, Mata Ta Nemi Saki A Kotun Musulunci, Miji Yace Ta Biya Kuɗi

  • Yusuf Muhammad, ɗan shekara 45 a duniya ya nemi Kotu ta umarci matarsa dake son su rabu ta biya shi miliyan N1.6m
  • Matar, wacce ta amince zata biya sadakin N30,000 ta shaida wa Kotu cewa ta gaji da auren, bata son fara saɓa wa Allah
  • Bayan sauraron kowane ɓangare Alƙalin Kotun ya ɗage zaman zuwa 12 ga watan Satumba, 2022

Kaduna - Wani Mutumi ɗan kimanin shekara 45 a duniya, Yusuf Muhammad, ranar Litinini, ya roki Kotun Shari'ar Musulunci dake zama a Magajin Gari, Kaduna, ta umarci Matarsa ta biya miliyan N1.6m kafin ya saketa.

Muhammad, ya gabatar da bukatarsa ne biyo bayan matar, Murjanatu Nasir, ta nemi Kotu ta yi amfaani da Khul'i, wato fansar kai a Musulunci wajen raba aurensu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Buhari Tace Ta Magance Mafi Munin Matsalar Tsaro a Najeriya

Matsalolin aure.
Bana Son Saɓa Wa Allah, Mata Ta Nemi Saki A Kotun Musulunci, Miji Yace Ta Biya Kuɗi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun da fari, Murjanatu ta yi alƙawari cewa zata maida wa Muhammada sadakin N30,000 da ya biya lokacin aurenta.

Sai dai, da yake bayani a gaban Kotu, magidancin yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"N50,000 na biya sadaki ba N30,000 ba kamar yadda ta faɗa kuma aurenta ya dakatar da N35,000 da 'yan uwana suke bani alawus duk wata sakamakon rashin lafiya."
"Tun da muka yi aure a 2018, 'yan uwana suka daina turo mun kuɗin alawus ɗin wata-wata saboda na aureta, saboda haka ta biya waɗan nan kuɗaɗen kafin na saketa."

Bana son saɓon Allah - Murjanatu

Matar ta bakin lauyanta, Abubakar Abdullahi, ta shaida wa Kotu cewa ba su yi wata yarjejeniya da shi cewa zata biya shi wasu kuɗaɗe ba.

"Bana son cigaba da zaman auren nan saboda bana son saɓa wa Allah (SWT)," inji Murjanatu.

Kara karanta wannan

Akan N1,500 na kudin wutan lantarki, wani ya bindige kaninsa har lahira

Alƙalin Kotun, mai shari'a Malam Rilwanu Kyaudai, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 15 ga watan Satumba, 2022 domin baiwa matar damar gabatar da shaidun.

A eani labarin kuma Saurayi Da Budurwa da Suka Fara Soyayya A Makarantar Firamare Sun Yi Aure, Hotunan Bikinsu Ya Yadu

Yayin da wasu ke shafe tsawon rayuwarsu wajen neman masoyi na gaskiya, wani saurayi da budurwarsa da suka hadu a makarantar firamare sun shiga daga ciki a wani kayataccen biki.

Brianna Ragbeer da Romane Cameron sun shiga babbar makaranta tare inda suka zama masoyan usuli a makarantar sakandare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262