Ruwa Yayi Awon Gaba da Sama da 'Yan Boko Haram 70 Sakamakon Luguden Sojojin Najeriya
- Sama da mayakan ta'addancin Boko Haram 70 ne suka rasa rayukansu sakamakon neman tserewa daga luguden sojin Najeriya da suka yi
- An gano cewa, sojojin Najeriya sun halaka 'yan ta'adda sama da 20 a kauyen Sheruri dake bama amma wasu sun tsere tare da kokarin ketare rafi
- Babu zato balle tsammani, ruwan yayi awon gaba da su inda aka samu gawawwakin sama da 50 daga ciki yayin da ake cigaba da neman sauran a ruwan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Borno - Sama da mmutum 70 da ake zargin 'yan Boko Haram ne ruwa yayi awon gaba da su a a wani rafi bayan luguden wutan da dakarun Operation Hadin Kai suka yi a jihar Borno, majiyoyi suka tabbatar.
An tattaro cewa, sojojin Najeriya tare da hadin guiwar kungiyar tsaron farar hula, JTF, sun halaka sama da 'yan ta'addan Boko Haram 20 a kauyen Sheruri dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno a ranar Alhamis.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiyoyi sun ce bayan farmakin Sheruri, wadanda suka tseren ruwa yayi awon gaba da su a rafin dake kusa da kauyen Dipchari dake karamar hukumar Bama a ranar Juma'a, Daily Trust ta rahoto.
"'Yan ta'addan sun tafka mummunar asara, sun rasa rayukan sama da mayaka 70 a kusa da kauyen Dipchari. A halin yanzu da muke magana, mutane da yawa daga cikin mayakan babu su babu dalilinsu," majiyar tsaro ta tabbatar.
"Da safiyar yau wurin karfe 8:30 na safe suka yi jana'izar sama da mayaka 50 a kauyen Dipchari kuma suna cigaba da neman gawawwakin sauran 'yan ta'addan.
“Sun samo gawawwaki masu yawa daga rafin amma har yanzu akwai mayakan da ba a gani ba," majiyar tace.
Har yanzu babu takardar da ta fito a hukumance daga rundunar sojin Najeriya kafin rubuta wannan rahoton, amma jama'a da yawa daga yankin sun tabbatar da wannan cigaban.
Rundunar sojin Najeriya na samun manyan nasarori a cikin kwanakin nan a sassan kasar nan.
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kwashe Jama'a
A wani labari na daban, 'yan bindiga a ranar Juma'a sun sace masallata masu tarin yawa daga Masallacin Juma'a na yankin Zugu dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun boye bidigoginsu a cikin kayansu kuma suka shiga masallacin yayin da liman yake dab da fara huduba, Daily Trust ta rahoto.
Asali: Legit.ng