Kano: Jami'an Hisbah sun damke mabarata 648 a tituna
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke mabarata 648 a birnin Kano sakamakon zarginsu da take da karya dokokin haramta bara a titunan jihar tun daga watan Fabrairu.
Kakakin rundunar hukumar Hisbah, Lawan Ibrahim, ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a yankunan Bata da ke kan babban titin Murtala Muhammed, asibitin Nasarawa, filin jirgin kasa da kuma wurin Yahuza Suya.
Ibrahim ya ce hukumar za ta ci gaba da kama mabarata wadanda suka ki bin doka a jihar, jaridar Daily Trust ta wallafa.
"Sai mun mayar da birnin Kano babu mabaraci ko daya. Wadanda aka kama duk an gama tantancesu kuma wadanda kamun farko ne za a mika su ga 'yan uwansu.
"Wadanda kuwa ba wannan bane karon kama su na farko, za a gurfanar da su gaban kotu," yace.
KU KARANTA: Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 14 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto
KU KARANTA: Abinda muke bukata domin magance ta'addanci da 'yan bindiga - CAS
Idan za mu tuna, a watan Mayu ne gwamnatin jihar Kano ta haramta Almajiranci a jiharta kuma ta lashi takobin cewa duk mahaifin da ya tura dansa Almajirci zai gurfana gaban kotu.
A cewar The Sun, Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya alanta akan ne ranar Laraba yayinda yake hira da manema labarai a gidan gwamnatin jihar.
Amma dai, gwamnan ya gindaya sharruda da ya wajaba a cika ga duk wanda ke son tara yara don karatun Allo.
Ganduje ya jaddada cewa wajibi ne manhajin karatun ya hada da ilimin Boko kuma wajibi ne malami ya tanadi azuzuwa, wuraren kwana, da isasshen abinci saboda kada yaran su fita bara.
Yace: "Gwamnatin jihar ba zata lamunci Almajiranci a jihar ba. Wajibi ne yara su kasance a makaranta.
"Wajibi ne makarantar ta bi ka'idojin makaratun Boko; wajibi ne a samu kwararrun malamai, a rika rubuta jarabawa, da kuma bibiya."
"Muna tabbatarwa al'ummar jihar cewa ana karantar da ilimin addini a makarantunmu na Boko kuma muna daukan kwararrun Malamai."
Ya kara da cewa kada hankalin Malaman makarantun Allo ya tashi saboda ba wai ana kokarin kwace musu aiki bane, gwamnatin jihar na shirye da daukansu aiki sashen ilimin jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng