Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kwashe Jama'a

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kwashe Jama'a

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki masallacin Juma'a a yankin Zugu dake karamar hukumar Zamfara inda suka sace masu sallah
  • An gano cewa, 'yan bindigan sun shiga masallacin tare da tattara jama'a ana dab da fara huduba inda suka shige daji da su
  • Kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana, sun yi garkuwa da muezzin amma Liman ya sha da kyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - 'Yan bindiga a ranar Juma'a sun sace masallata masu tarin yawa daga Masallacin Juma'a na yankin Zugu dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara,

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun boye bidigoginsu a cikin kayansu kuma suka shiga masallacin yayin da liman yake dab da fara huduba, Daily Trust ta rahoto.

Labari da Dumi
Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Cikin Masallaci a Zamfara, Sun Kwashe Jama'a
Asali: Original

Maharan sun sanar da wadanda ke wajen Masallacin da su shiga ciki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Ta'adda Sun Kai Wa Ayarin Motoccin Hajiya Zainab Gummi Hari A Zamfara

"A lokacin da suka zagaye masallacin, sun bukaci duk wadanda ke wajen masallacin da su shiga ciki cewa sun zo ne domin tattauna kan yadda zasu sako wasu mutanen dake hannunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu wanda ya gansu da bindigogi kuma mutane da yawa sun kallesu a matsayin masu bauta. Babu wanda ya mayar da hankali kansu saboda sun boye bindigoginsu.
"Sai dai, jim kafdan bayan sun shiga cikin masallacin suka fito da bindigoginsu tare da yin harbin gargadi.
"Sun jagoranci masu bautar zuwa cikin daji amma wasu masu bautar sun yi nasarar arcewa daga masallacin. An sace Muezzin amma Liman ya sha da kyar," cewar wata majiya.

Abubakar mazaunin yankin ya kara da cewa:

"Wasu daga cikin wadanda ke wajen masallacin duk an yi garkuwa da su saboda basu san 'yan bindigan sun tsaya a wurare daban-daban a wajen masallacin ba. Sun yi harbe-harbe a iska sannan suka tarkata jama'a zuwa daji."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani kasurgumin dillalin bindiga dauke da makamai zai tafi Zamfara

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, yace har yanzu bai samu rahoton farmakin ba amma ya yi alawakrin karin bayani idan ya samu daga bisani.

'Yan Sanda Sun Magantu Kan Batun Kama Bakin Haure Suna Dillancin Makamai da Helikwafta

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Niger tace bata kama wasu bakin haure a kasar nan suna rarraba makamai ta jirgin sama ga 'yan bindiga a jihar ba.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Monday Kurya ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna a ranar Juma'a cewa, lamarin bai taba faruwa ba kowanne sashi na jihar.

Kurya ya kwatanta rahoton da labarin bogi dake yawo a soshiyal midiya saboda bai taba faruwa a jihar ba, Daily Nigerian ta rahoto hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng