Buhari ya Kara Alawus din Tafiye-tafiye: 250% na Manyan Sakatarorin Gwamnati, 128% na Ministoci
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin alawus din tafiye-tafiyen aiki na ma'aikatan tarayya
- Wannan karin alawus din zai shafi ma'aikata tun daga mataki na daya har zuwa na 17 a tarayya
- Ministoci, SGF, HCFS da makamantansu zasu samun karin 128% yayin da manyan sakatarorin gwamnati zasu samu karin 250%
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince da karin alawus din yawon aiki, DTA, ga ministoci, manyan sakatarorin gwamnati da ma'aikatan gwamnati daga mataki na 1 zuwa 17.
Alawus din yawon aiki, DTA, yana nufin kudin da gwamnati a ke biyan ma'aikacin da yayi tafiyar aiki.
Jaridar TheCable ta rahoto cewa, sabon amincewa da sabon alawus din ya bayyana ne a wata takarda mai kwanan wata 31 ga Augusta kuma an mika ta ne ga Ekpo Nta, shugaban hukumar albashi ta kasa.
Nta yace sabon alawus din zai fara aiki a ranar 1 ga watan Satumban wannan shekarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Shugaban kasar Najeriya ya amince da karin alawus din tafiye-tafiye wanda zai shafi manyan sakatarorin gwamnati daga N20,000 zuwa N70,000 da ministoci, sakataran gwamnatin tarayya, HCFS, da makamantansu daga N35,000 zuwa N80,000," takardar tace.
"Dukkan tambaya dake da alaka da wannan takardar a miko ta ga hukumar," takardar ta kara da cewa.
Ga bayanin sabon karin DTA din kamar yafdda yake kunshe a takardar:
• Mataki (GL) 01-04 da makamantansu – N10,000
• GL 05-06 da makamantansu – N15,000
• GL 07-10 da makamantansu – N17,500
• GL 12-13 da makamantansu – N20,000
• GL 14-15 da makamantansu – N25,000
• GL 16-17 da makamantansu– N37,500
• Manyan sakatarori da makamantansu – N70,000
• Minista/SGF/HCSF/makamantansu – N80,000
A watan Augsuta, shugaban kasa yace akwai bukatar gaggauta sake duba albashin ma;iakatan gwamnatin tarayya sakamakon hauhawar farashin kayayyaki a fadin duniya.
Hauhawar farashin kayayyaki yayi tashin gwauron zabi da kashi 19.64 a Yulin 2022 daga 18.60 a watan da ya gabace shi, kamar yadda CPI ta tabbatar.
Buhari ya Gwangwaje Yayan Uwargidansa da babban Mukami a CBN
A wani labari na daban, wani rahoto daga jaridar Daily Nigerian ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Halilu matsayin sabon manajan daraktan Nigerian Security Printing and Minting Company, NSPMC.
Legit.ng ta tattaro cewa, Halilu yayan uwargidan shugaban kasa ne, Aisha Buhari.
Amintar shugaban kasan kan nadin Halilu matsayin manajan daraktan kamfanin buga kudin na Najeriya ya biyo bayan shawarar gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Asali: Legit.ng