Rushewar Ginin Kano: Tinubu ya Aike wa Ganduje Wasikar Jaje
- 'Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Ganduje jaje kan rushewar ginin kasuwar Kano
- A wasikar da Tinubu ya aike wa gwamnan Kanon, ya jajanta wa 'yan uwa da iyalan wadanda ibtila'in ya ritsa da su tare da fatan zasu rungumi hakan matsayin kaddara
- Tinubu yayi kira ga gwamnati da ta kula da wadanda suka jigata sakamakon hatsarin inda yace a binciki tushen lamarin don gujewa sake faruwar hakan
Kano - 'Dan takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan rayukansu da aka rasa a rushewar gini mai hawa uku na kasuwar Beirut a jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a wasikar da Tinubu ya rubuta zuwa Gwamna Ganduje mai kwanan wata 31 ga Augustan 2022, ya bayyana matukar damuwarsa da tausayawa kan mummunan al'amarin da ya faru.
Ya kara da yi wa wadanda suka samu rauni fatan samun lafiya.
"Rushewar bene mai hawa uku da ake ginawa abu ne mai taba rai. Wadanda suka suka rasa rayukansu bai dace su rasu a wannan halin ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A yayin fatan Allah ya ji kan wadanda suka rasa rayukansu, ina jajanta wa iyalansu da 'yan uwansu. Ina kira garesu da su dauka hakuri tare da rungumar lamarin matsayin kaddara daga Allah.
"Ina jajanta wa wadanda suka samu rauni tare da fatan warakarsu cikin gaggawa. Ina kira ga gwamnati da ta cigaba da tabbatar da an kula da wadanda suka samu rauni.
"A tsananta kokarin ceto wadanda ginin ya rusa da su har sai an fitar da kowa.
"Bari in yi amfani da wannan damar wurin jajanta wa shugaba da hukumar kasuwar da 'yan kasuwan kan hatsarin da asarar da suka tafka.
"A yayin kira ga gwamnati da ta gaggauta bincike kan lamarin da ya kawo rushewar ginin domin gujewa faruwar lamarin a nan gaba, ina fata da addu'ar wannan mummunan lamarin bai sake faruwa ba."
Jonathan: Najeriya Ta Kama Hanyar Koma Wa Mulkin Kama-Karya
A wani labari na daban, tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya ce Najeriya ta kama hanyar gangarawa mulkin kama karya.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wurin taron bikin cika shekaru 70 na Bishop din cocin Katolika na Sokoto, Matthew Kukah, da aka yi a Sheraton Hotel a Abuja.
Asali: Legit.ng