Wani Dan Jihar Anambra Ya Harbe Kaninsa Har Lahira Saboda N1,500 Kudin Wutar Lantarki
- Wani mummunan lamari ya faru, wani mutum ya bindige kaninsa saboda N1,500 na kudin wutar lantarki
- Rundunar 'yan sanda ta yi nasarar kame mutumin tare da matarsa da a halin yanzu suke tsare a hannunsu
- Ya zuwa yanzu, rundunar 'yan sanda ta ba da umarnin tura mutumin zuwa zashen bincike don ci gaba da bincike
Nnewi, jihar Anambra - Kudin wutar lantarki N1,500 ta hada 'yan uwa biyu fada a jihar Anambra, daya ya fusata ya dirkawa daya bindiga.
Peter Orji ya kashe kaninsa mai suna Godwin ne yayin da gardama ta barke tsakaninsu a gidansu dake Uruagu a karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.
Jaridar Punch ruwaito cewa ’yan uwan biyu suna cikin zaman zamansu ne lokacin da suka fara kai ruwa rana saboda Peter ya ki biyan N1,500 na wuta da yake biya a duk wata.
Domin tursasa masa biyan kudin, Godwin ya yanke wutar da ke kai wa ga bangaren Peter, lamarin da ya tunzura shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wata majiya a unguwar ta ce yayin da Peter ya fusata, ya dira dakin kanin nasa, inda ya fito da bindiga da dirke shi.
Bayan sheke kaninsa nasa, Peter ya gaggauta mika kansa ga ofishin 'yan sanda dake kusa da yankin don gudun fushin jama'a da matakin da za su iya dauka.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an kamo wanda ake zargin ne sabanin labarin da ke cewa ya mika kansa ne, rahoton Daily Trust.
Ikenga ya kuma ce, an fara kwamushe matar Peter kafin daga bisani aka kamo shi a hada su a magarkamar 'yan sanda.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Echeng Echeng, ya ba da umarnin a mika batun ga shashen binciken manyan laifuka na jihar domin fara cikakken bincike.
Matashi Ya Tattaro Mota da Wayoyin Uban Gidansa Ya Siyar, Zai Tafi Turai
A wani labarin, wani matashi dan shekaru 21 mai suna Temple Samuel ya shiga komar rundunar 'yan sandan jihar Legas bisa laifin sata tare da siyar da mota kirar Lexus ES 330 ta ubangidansa a unguwar Ogba dake jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a wata wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Legas, Premium Times ta ruwaito.
Ya shaida cewa, jami’an rundunar Rapid Response Squad (RRS) na jihar Legas ne suka kama matashin tare da abokansa uku.
Asali: Legit.ng