Allah Yayi wa Tsohon Jakadan Najeriya a Kasar Saudi Arabia, Imam, Rasuwa
- Allah yayi wa Alhaji AbdulKadir Imam, tsohon jakadan Najeriya a kasar Saudi Arabia, rasuwa a ranar Alhamis
- Imam ya rasu yana da shekaru 90 a duniya a garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara kuma za a yi jana'izarsa a yau
- Imam ya taba yin jakaden Najeriya a kasashen Saudi Arabia, Libya, Masar, Jamus, Lebanon da Poland
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ilorin, Kwara - Tsohon jakaden Najeriya a kasar Saudi Arabia, Alhaji Abdulkadir Imam, ya kwanta dama.
Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, Imam ya rasu a garinsu na Ilorin dake jihar Kwara a yayin da yake da shekaru 90 a duniya.
Daya daga cikin 'ya'yan mamacin, Dr AbdulRazak Imam, ya tabbatar da rasuwar tsohon jakaden.
Yace za a birne mahaifinsa a yau Juma'a a daya daga cikin gidajensa dake GRA a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Imam a lokuta da dama ya kasance ambasadan Najeriya a kasashen Saudi Arabia, Jamus, Libya, Misra, Lebanon da Poland.
Ya yi aiki a matsayin daraktan hukumar hajji ta kasa.
Allah Yayi wa Tukur Othman, Tsohon Manajan Daraktan Jaridar New Nigerian, Rasuwa
A wani labari na daban, tsohon manajan daraktan jaridar New Nigerian, Malam Tukur Othman, ya riga mu gidan gaskiya. Ya rasu a asibitin Garkuwa dake Kaduna a sa'o'in farko na ranar Juma'a.
Daily Trust ta rahoto cewa, tsohon manajan daraktan NNN din shi ne zababben mai bada shawara a fannin rubutu na jaridar Desert Herald a Kaduna.
Mawallafi kuma shugaban kamfanin jaridar, Malam Tukur Mamu, mai sarautar Dan-Iyan Fika ne ya sanar da rasuwar a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a da safe.
"A yayin da muke cigaba da godiya kan ayyukansa na kishin kasa da yake mana, Najeriya da dukkan masana'antar jarida, ina mika sakon ta'aziyyata ga dukkan iyalansa da masoyansa a madadin FUZA Communication Services Ltd. Allah yasa doguwar jinyar da yayi ta zame masa kaffara kuma ya samu gidan Aljannar Firdausi," yace.
Asali: Legit.ng