Allah Yayi wa Tukur Othman, Tsohon Manajan Daraktan Jaridar New Nigerian, Rasuwa

Allah Yayi wa Tukur Othman, Tsohon Manajan Daraktan Jaridar New Nigerian, Rasuwa

  • Tukur Othman, tsohon manajan daraktan jarida New Nigerian, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma'a
  • Ya rasu a sa'o'in farko na yau a asibitin Garkuwa dake cikin garin Kaduna bayan doguwar jinya da yayi fama da ita
  • Tukur Othman ya rasu inda ya bar mata biyu na aure tare da 'ya'ya 16 a duniya, an kuma yi jana'izarsa kamar yadda Musulunci ya tanadar

Kaduna - Tsohon manajan daraktan jaridar New Nigerian, Malam Tukur Othman, ya riga mu gidan gaskiya. Ya rasu a asibitin Garkuwa dake Kaduna a sa'o'in farko na ranar Juma'a.

Daily Trust ta rahoto cewa, tsohon manajan daraktan NNN din shi ne zababben mai bada shawara a fannin rubutu na jaridar Desert Herald a Kaduna.

Tukur Othman
Allah Yayi wa Tukur Othman, Tsohon Manajan Daraktan Jaridar New Nigerian, Rasuwa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mawallafi kuma shugaban kamfanin jaridar, Malam Tukur Mamu, mai sarautar Dan-Iyan Fika ne ya sanar da rasuwar a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a da safe.

Kara karanta wannan

Rarara Ya Rabu Da Tsohon Mai Gidansa, Ya Koma Bangaren Sharada

“A yayin da muke cigaba da godiya kan ayyukansa na kishin kasa da yake mana, Najeriya da dukkan masana'antar jarida, ina mika sakon ta'aziyyata ga dukkan iyalansa da masoyansa a madadin FUZA Communication Services Ltd. Allah yasa doguwar jinyar da yayi ta zame masa kaffara kuma ya samu gidan Aljannar Firdausi," yace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya sanar da cewa za a yi jana'izarsa a masallacin Misbahu dake Unguwan Rimi, Kadaria, Kaduna bayan sallar Juma'a.

Tsohon manajan daraktan ya rasu ya bar matan aure biyu da 'ya'ya 16.

Har Abada Zan Kaunace Ki: Mawaki Eedris Abdulkareem ga Matarsa da ta Bashi Kyautar Koda

A wani labari na daban, fitaccen mawakin gambara, Eedriss Abdulkareem, ya mika godiyarsa ga matarsa Yetunde kan bashi kyautar kodarta da tayi kuma aka samu nasarar yi masa dashe.

Mawakin ya bayyana godiyarsa ne a wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram a ranar Laraba inda ya kara da cewa zai kaunaceta tare da sonta a koda yaushe.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Allah Ya Yiwa Kauran Katsina Kuma Hakimin Rimi, Nuhu Abdulkadir, Rasuwa

Idan za tuna, kamfaninsa na nishadantarwa ya bada bayani kan lafiyar mawakin a ranar Litinin.

A wata takarda da Honarabul Myke Pam ya fitar, yace an samu nasarar yi wa mawakin dashen kodar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel