Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Matashi Dan Shekaru 15, Ya Ce Mawaki Davido Ba Zai Iya Siyan Irinsa Ba
- Wani matashin yaro ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ya baje kolin wani gida da yace mallakinsa ne
- Dan Najeriyan ya rubuta cewa shekarunsa 15 kuma yana rayuwa a inda mawaki Davido ba zai iya siya ba
- Hakan bai yiwa masoyan Davido dadi ba inda suka caccake shi a sashin sharhi tare da kushe gidan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Wani matashi dan shekara 15 ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ya nuna katafaren gidansa cike da tunkaho.
Matashin da ke ikirarin yafi kowa kyau a Abuja ya je shafinsa na TikTok don wallafa bidiyonsa yana zagaye tare da nuna tsaruwan cikin gidan.
Ya yi shagube ga mawaki Davido. Rubutu da ya yi a jikin bidiyon da ya wallafa ya ce:
“Yaro dan shekara 15 da ke rayuwa a inda Davido ba zai taba iya siya ba.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya fusata masoyan Davido wadanda suka caccaki shi. Sun kuma kushe kyawun gidan.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
Pack-me ya ce:
“Wa ya fada maka cewa Davido ba zai iya siyansa ba???
“Na dai tayaka murnar wannan nasara taka.”
Regina Gold820 ta ce:
“Yana nufin Davido ba zai taba siyan irin wannan gidan ba faaaa ku dai ne baku fahimci abun da ya fada ba.”
Delly Nuel ta ce:
“Lol, an sanmu da mutunta na gaba damu a Najeriya Don haka kaima kayi haka dan Allah, hakan zai kara maka hankali ne kawai.”
Yan Uwansa Sun Cika Alkawari: Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Dan Najeriya Mazaunin Dubai Ya Ja Hankali
A gefe guda, wani matashi dan Najeriya wanda ya dawo gida kwanan nan daga Dubai ya baje kolin cikin kuryar katafaren gidansa.
Matashin dai yana ta turowa yan uwansa kudi domin su taimaka su gina masa gida yayin da shi kuma yake aiki tukuru a kasar Dubai.
Cikin sa’a, yan uwan nasa sun rike amana sannan basu yi almubazaranci da kudinsa ba, don ya dawo ya tarar da wani katafaren gida.
Asali: Legit.ng