Ya Farka A Kidime: Bidiyon Yadda Budurwa Ta Sa Aska Ta Gwaguye Gashin Saurayinta Yana Cikin Barci

Ya Farka A Kidime: Bidiyon Yadda Budurwa Ta Sa Aska Ta Gwaguye Gashin Saurayinta Yana Cikin Barci

  • Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuno yadda budurwa ta saka aska ta gwaguyewa saurayinta sumansa yana tsaka da bacci
  • Bayan ta aske rabin gashin, sai ta tashe shi daga baccin don ya ga sabon kamminsa kuma ya gigita sosai
  • Da take kare kanta, budurwar ta nunawa saurayin nata cewa tana son yi masa irin askin wani shahararren dan wasa ne

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wata budurwa tana yiwa saurayinta aski yayin da yake sharar bacci sannan ta tashe shi bayan ta kammala aikinta.

Bidiyon wanda aka watsa kan TikTok ya nuno matashiyar rike da abun aski tana gwaguye gashin saurayin yayin da yake bacci.

Matashi
Ya Farka A Kidime: Bidiyon Yadda Budurwa Ta Sa Aska Ta Gwaguye Gashin Saurayinta Yana Cikin Bacci Hoto: TikTok/@flashxgangz
Asali: UGC

Bayan ta gwaguye rabin gashin, sai ta tashe shi domin ya ga sabon kamanninsa. Mutumin ya shiga dimuwa bayan ya kalli kansa a madubi.

Kara karanta wannan

Idanun Wani Sun Bude: Yadda Yan Mata Suka Warware Surkullen Da Kawarsu Ta Yiwa Saurayinta, Ta Daure Shi A Kwalba

Yana ta gudu a dakin daga kusurwa zuwa kusurwa yana ihu cikin jimami yana tambayar budurwar kan dalilinta na lalata masa gashinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, budurwar ta nuna masa hoton wani shahararren dan wasa wanda ke dauke da irin askin sannan ta yi masa bayanin cewa irin shi take son yi masa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Precious ta ce:

"Wacce irin budurwa ce wannan yanzu gashi yana da dan uwa...askin ya yi maka kyau dan uwa."

maxlewisj ya ce:

"Ya aka yi bai tashi ba...Ina tashi idan yarana suka yi tusa a dakin da ke kusa dani."

Orpeyemi ya ce:

"Ko shakka babu zan aikata mata irin haka ita ma kuma idan ta fusata rabuwa kai tsaye."

Yadda Yan Mata Suka Warware Surkullen Da Kawarsu Ta Yiwa Saurayinta, Ta Daure Shi A Kwalba

Kara karanta wannan

Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Aiki A Kasar Waje, Budurwa Ta Dawo Gida Najeriya, Ta Zama Mai Jiran Shago

A wani labarin, wata budurwa da ba a gane ko wacece ba ta sha caccaka a wajen kawayenta a soshiyal midiya kan saka sunan saurayinta a da tayi a cikin kwalba.

A cewar yan matan a wani bidiyo da ya yadu, sun yi ikirarin cewa budurwar wacce ta kasance kawarsu ta daddaure kwalban kafin ta jefa shi a cikin rafi.

Yayin da suke kwancewa kawar tasu zani a kasuwa kan abun da ta aikata, sun koka cewa rayuwarsu suma tana cikin hatsari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel