Gwamnatin Tarayya Zata Bude Jami'o'i Duk Da Yajin Aikin ASUU

Gwamnatin Tarayya Zata Bude Jami'o'i Duk Da Yajin Aikin ASUU

  • Ministan Ilimi ya gayyaci shugabannin jami'o'in Najeriya Abuja don tattaunawa kan lamarin ASUU
  • Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnati na kokarin bude jami'o'i karfi da yaji tun da ASUU ta hakura
  • Kungiyar Malamai ASUU ta lashi takobin cewa sai an biya mambobinta albashi za su koma aiki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Alamu sun bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin bude jami'o'in Najeriya duk da yajin aikin kungiyar Malaman jami'a watau ASUU.

A cewar majiyoyi a ma'aikatar Ilimi, Malamai kadai ne ma'aikatan jami'an da suka rage basu komai aiki ba saboda tuni sauran ma'aikatan jami'a irinsu NASU, da SSANU sun janye daga yaji.

Majiyar tace:

"Akwai wasu Lakcarori dake son komawa aiki, saboda me za'a hanasu."
"Saboda me za'a hana masu son komawa aiki yin aikinsu?
Adamu Adamu
Gwamnatin Tarayya Zata Bude Jami'o'i Duk Da Yajin Aikin ASUU
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Wani abu zai faru, gwamnati ya share ASUU, ta kira ganawa da shugabannin jami'o'i

Ma'aikatar zata gana da Shugabannin jami'o'i

Wannan ya biyo bayan zaman da ma'aikatar Ilimi ta shirya da shugabannin jami'o'i ranar Talata mai zuwa.

Rahoton Vanguard a bayyana cewa za'ayi wannan zama ne a ofishin hukumar jami'o'in Najeriya NUC dake Abuja tare da Ministan Ilimi, Adamu Adamu.

A wasikar da aka aikewa shugabannin jami'o'in mai lambar NUC/ES/138/VOL. 64/125, an yi zaman taken "Gayyata zuwa tattaunawa da Mai girma Ministan Ilimi Game da Yajin Aiki."

Wani sashen wasikar yace:

"A matsayinku na shugabannin jam'i'oi, yajin aiki ya yi sanadiyar rufe makarantu tun ranar 14 ga Febrairu, 2022."
"Kuna sane da cewa sauran kungiyoyi sun janye daga yajin aiki run ranar 24 ga Agusta, yayinda ASUU taki har yanzu ana sauraronta."
"Ya zama wajibi a sanar da shugabannin jami'o'i kan matakai da shawarin da gwamnatin tarayya ta dauka kan yadda za'a shawo kan lamarin."

Jami'ar IBB Dake Lapai Jihar Neja Ta Janye Daga Yajin Aikin ASUU, Tace Dalibai Su Koma Aji

Kara karanta wannan

Da Dumi: Jami'ar IBB Dake Lapai Jihar Neja Ta Janye Daga Yajin Aikin ASUU, Tace Dalibai Su Koma Aji

A wani labarin kuwa, Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida dake garin Lapai, jihar Neja ta sanar da daukacin dalibai da Malamai su gaggauta komawa aji ba tare da bata lokacin.

Kwamitin Shugabannin makarantar ta bayyana hakan ne a jawabin da mataimakin Rajistran ya fitar ranar Talata, 30 ga watan Satumba, 2022.

Ya bayyana cewa sun yanke shawarar haka bayan zaman da majalisar zartaswa na jam'iyar tayi ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel