Zan Siya Gida Kwanan nan A Birnin Lagas: In ji Mai Sana’ar Kifi, Mutane Sun Karfafa Mata Gwiwa
- Wata matashiyar yar Najeriya da ke siyar da kifi a yanar gizo ta baje kolin sana’arta yayin da take burin yin nasara wata rana
- Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon budurwar sun karfafa mata gwiwar cewa mafarkinta zai zama gaskiya idan ta jajirce
- Daya daga cikin bidiyoyinta ya nunota zaune a gaban tiren busasshen kifi a cikin kasuwa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagas - Wata budurwa yar Najeriya wacce ke alfahari da sana’arta na siyar da busasshen kifi a bidiyoyinta na TikTok ta bayyana mafarkinta cike da karfin guiwa.
A cikin bidiyon, budurwar ta sanar da wadanda ke ganin ba za ta cimma nasara ba a sana’ar kifinta cewa:
“Nan ba da dadewa ba zan siya gida a birnin Lagas.”
Ta girgije cike da farin ciki
Yayin da take rawa a wajen da take gasa kifi, sauran matane da ke wajen suna ta kallonta. Mutane da dama sun yi kira gareta a kan ta kara himma don babu abun da ya fi karfin Allah.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani nazari kan shafinta ya nuna cewa tana son habbaka kasuwancin kifinta a yanar gizo.
Kalli bidiyon a kasa:
Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin mutane a kasa:
user8824043150619 ya ce:
“Ki yi farin ciki yar’uwata. Kina da kasuwanci naki na kanki. Allah ya albarkaceki daga wannan sana’ar Amin. INA KAUNARKI.”
dacyncynthiky ya ce:
“Allah ya albarkaci nemanki.”
Ayomide ta ce:
“kawai ki ci gaba da aiki tukuru.”
Ashley ta ce:
“Allah ya albarkaci aikin hannunki.”
Ina Samun Miliyan N2 A Sati 2: Dalibin Najeriya Da Yajin Aikin ASUU Ya Ritsa Da Shi Ya Kafa Sana’a
A wani labarin, wani matashin dan Najeriya ya nuna cewa yajin aikin malaman jami’o’i na ASUU da ke gudana a yanzu haka alkhairi ne a bangarensa domin ya yi amfani da wannan damar wajen bunkasa kasuwancinsa.
A cikin wani bidiyo, mutumin ya bayyana cewa ya kafa kasuwanci a lokacin yajin aikin kuma ya fara koyon yadda ake bunkasa sana’a ta hanyar amfani da bidiyoyi.
Don ganin kasuwancinsa ya habbaka a yanar gizo, dalibin ya bayyana cewa ya kashe jimilar N200,000 kan samawa sana’ar suna.
Asali: Legit.ng