Kotun Tarayya Ta Sake Hana Bayar da Belin Abba Kyari da Wasu Mutum Hudu

Kotun Tarayya Ta Sake Hana Bayar da Belin Abba Kyari da Wasu Mutum Hudu

  • Babbar Kotun tarayya ta sake watsi da bukatar ba da belin Abba Kyari, da abokan harkallarsa hudu yau Talata
  • Alkalin Kotun mai shari'a Emeka Nwite, ya ce waɗan da ake zargin sun gaza gabatar da gamsassun hujjoji
  • Hukumar NDLEA ta ƙasa ta gurfanar da Abba Kyari da wasu mutum huɗu bisa tuhumar safarar miyagun kwayoyi

Abuja - Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta ƙi amincewa da ba da Belin dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari, da wasu mutum huɗu.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta gurfanar da Kyari da wasu mutum hudu gaban Kotu ne kan zargin safarar miyagun kwayoyi.

Abba Kyari.
Kotun Tarayya Ta Sake Hana Bayar da Belin Abba Kyari da Wasu Mutum Hudu Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels TV ta ruwaito cewa a ranar 7 ga watan Maris, 2022, NDLEA ta fara gurfanar da Abba Kyari (wanda ake tuhuma na farko) da wasu mutum Shida kan zargin harkallar shigo da Hodar Iblis.

Kara karanta wannan

Sunaye: Za a yi Gagarumin Ruwan Sama na Tsawon Kwanaki 4 a Jihohi 6, NiMet

An gurfanar da shi ne tare da wasu jami'an 'yan sanda huɗu da aka dakatar waɗan da suka haɗa da, ACP Sunday Ubia, ASP James, Insufekta Simon Agirigba da Insufekta John Nuhu, a matsayin na 2 zuwa na 5 da ake tuhuma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake yanke hukunci kan neman belin, Mai shari'a Emeka Nwite, ya ce waɗan ake zargin sun gaza gabatar da isassun kayayyaki da gamsassun hujjoji da zasu sanya Kotu ta amince da bukatar belin.

Bisa haka, Mai Shari'a Nwite, ya tabbatar da hukuncin farko da kotu ta yanke ranar 28 ga watan Maris, 2022 wanda ya umarci gaggauta shari'ar har a ƙare.

Kotu zaɓi ranar fara Shari'ar Kyari

Bayan haka, Alkalin Kotun ya zaɓi ranarkun 19, 20 da 21 ga watan Oktoba, 2022 a matsayin lokacin sauraron shari'ar Abba Kyari, da sauran jami'an yan sanda hudu da ake zargin abokan harkallarsa ne.

Kara karanta wannan

Sunayen ‘Yan Siyasa da Bara-Gurbi da Buhari Ya Nemi Ya Cusa a INEC Sun Fito Fili

A halin yanzun, waɗan da ake zargin zasu cigaba da zama a gidan gyaran Halin Kuje dake birnin tarayya Abuja, gabanin zuwan ranakun shari'ar a watan Oktoba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin kuma kun ji cewa Kotu ta yi fatali da bukatar gwamnatin shugaba Buhari na izinin tasa keyar Kyari zuwa Amurka

Alkalin Kotun da ke zamanta a Abuja, Inyang Ekwo, ya ce dokar Najeriya ta haramta miƙa wanda ake zargi wata ƙasa yayin da yake fama da shari'a a gida.

Amurka na zargin da hannun Abba Kyari a wata damfarar makudan kuɗaɗe da Ramon Abbas ya yi wa wani ɗan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262