Rashin Soyayya: Kotu Ta Raba Auren Shekara Biyu a Abuja Kan Abu Guda
- Wata Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta raba auren shekara biyu tsakanin Aisha da Hassan bisa hujjar rashin soyayya
- Matar ta shaida wa Kotu bata ƙaunar ta sake ganin mijinta har abada domin ba ta jin daɗin zama da shi kwata-kwata
- Magidancin ya roki a ba shi mako biyu ya yi shawara amma hakan ba ta faru ba saboda zubar hawayen Aisha
Abuja - Wata Kotu a Kubwa, birnin tarayya Abuja ta raba auren da ya shafe shekara biyu tsakanin wata ma'aikaciya, Aisha Ari, da mai gidanta, Ibrahim Hassan, saboda rashin soyayya.
Alƙalin Kotun, mai shari'a Malam Muhammad Adamu, ya raba auren kamar yadda Shari'ar Musulunci ta tanada bayan Aisha ta nemi saki a Kotu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Adamu ya kuma umarci Aisha ta yi 'Iddah' watau ta kula da yin jinin al'ada sau uku daga ranar da Kotu ta yanke hukunci kafin ta sake yin wani auren.
Yadda zaman Kotun ya kasance
Aisha ta shaida wa Kotun cewa ba ta sake ganin Hassan ba tun zaman ƙarshe ranar 2 ga watan Agusta. Tun wannan lokaci bai yi wani yunkurin sulhu ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Matara ta ƙara da cewa ta daina ƙaunar mijinta kwata-kwata, wanda ta aura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
"Ban jin daɗin zama da shi, ina rokon Kotu ta raba auren mu saboda rashin soyayya," a cewar Aisha.
Hassan ya yi yunkurin neman a ba shi mako biyu domin ya shawarci iyayensa da surukansa kan batun amma hakan bata samu ba saboda Aisha ta barke da kuka tana faɗa wa Kotun bata son sake ganin Hassan har abada.
"Bana son ganin shi har abada, bana jin daɗin zama da shi. Yana da makullan gidan mu, ya je ya tattara kayansa ya bar mun gida."
A wani labarin kuma Ya Rabu Da Ni Saboda Na Shiga Aikin Soja, Jarumar Soja Tayi Magana Kan Tsohon Saurayinta
Wata kyakkayawar budurwa dake aikin Soja ta shiga duniyar TikTok da labarin abinda ya faru tsakaninta da saurayinta.
Budurwar ya saki hotunan kanta cikin kayan Sojojin Najeriya da kuma lokacin da take farar hula.
Asali: Legit.ng