Atiku Abubakar Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Kano

Atiku Abubakar Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Kano

  • Ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya baiwa mutanen da Ambaliya ta shafa a Kantin Kwari tallafin miliyan N50m
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ziyarci Kano ne domin karɓan tsohon gwamna, Malam Shekarau zuwa jam'iyyar PDP
  • A yau Litinin, Sanata Shekarau, ya tabbatar da sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa PDP a gidansa

Kano - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ba da tallafin Naira Miliyan N50m ga mutanen da Ambaliyar ruwa ta takaita a fitacciyar kasuwar nan, Kantin Kwari, da ke birnin Kano.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wata Ambaliyar ruwa sakamakon matsanancin ruwan sama ta lalata kayayyakin da suka kai na kimanin miliyan N200m a ƙasuwar.

Atiku Abubakar da gwamna Okowa.
Atiku Abubakar Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Kano Hoto: @atiku
Asali: Twitter

A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA), Ambaliyar ta shafi shagunan ƴan kasuwa kusan 200.

Kara karanta wannan

Bayan shiga PDP, Shekarau ya daukar wa Atiku wani alkawari mai girma a zaben 2023

Ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar PDP a zaɓen 2023 da wasu jiga-jigan jam'iyya na ƙasa sun ziyarci Kano ne domin karɓan Sanata Ibrahim Shekarau, wanda ya sauya sheka daga NNPP zuwa PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a gidan Shekarau, tsohon gwamnan Kano, Atiku ya ce:

"Kano sananniyar cibiyar kasuwanci ce da ke taka rawa a tattalin arziki, ina amfani da wannan damar wajen jajanta wa ƴan kasuwan da lamarin Ambaliyar ya taɓa sakamakon saukar ruwa kamar da bakin kwarya."
"Haka zalika ina mai amfani da wannan dama wajen ba da tallafin kuɗi Naira Miliyan N50m ga waɗan da wannan abu mara daɗi ya shafa."

Shekarau Ya koma PDP

Bayan watanni shida kacal da komawa NNPP mai kayan marmari, Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya tabbatar da komawa PDP a gidansa da ke Munduɓawa ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shekarau Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Bayan Wata 3 Rak a NNPP

Sanatan ya bayyana cewa tuni ya aike da wasiƙa ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, yana mai sanar mata da janye wa daga takarar Sanata karkashin NNPP, kamar yadda rahoton Daily Trust ta ruwaito

A wani labarin kuma kun ji cewa gwamna Wike na jihar Ribas ya yi tsokaci kan rikicinsa da Atiku, ya ce wani abu na gab da faruwa

Gwamnan Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ba abun da ya faru a jam'iyyar PDP amma nan ba da jimawa ba wani abu zai faru.

Wike wanda ke takun saƙa da Atiku, ɗan takarar shugaban kasa a PDP ya ce ba abinda zai razana shi wajen yin abinda ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262