Babbar Kotun Tarayya Ta Yi Watsi Da Bukatar FG Na Mika Abba Kyari Amurka

Babbar Kotun Tarayya Ta Yi Watsi Da Bukatar FG Na Mika Abba Kyari Amurka

  • Babbar Kotun tarayya ta yi fatali da bukatar FG da NDLEA na izinin miƙa Abba Kyari kasar Amurka ya fuskanci shari'a
  • Alkalin Kotun da ke zamanta a Abuja, Inyang Ekwo, ya ce dokar Najeriya ta haramta miƙa wanda ake zargi wata ƙasa yayin da yake fama da shari'a a gida
  • Amurka na zargin da hannun Abba Kyari a wata damfarar makudan kuɗaɗe da Ramon Abbas ya yi wa wani ɗan kasuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da bukatar gwamnatin tarayya na tasa keyar dakataccen mataimakin Kwamishinan yan sanda zuwa Amurka.

Alƙalin Kotun, mai shari'a Inyang Ekwo, shi ya yanke hukuncin kan ƙarar da Ministan Shari'a, Abubakar Malami da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) suka shigar.

DCP Abba Kyari.
Babbar Kotun Tarayya Ta Yi Watsi Da Bukatar FG Na Mika Abba Kyari Amurka Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Channels tv ta rahoto cewa, da yake yanke hukunci ranar Litinin, Alƙalin Kotun ya yi watsi da bukatar bisa hujjar cewa ƙarar ta gaza kuma tana da naƙasu.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: ASUU ta gama tattaunawa a Abuja, ta sake fitar da matsaya

Mai Shari'a Ekwo ya bayyana cewa sashi na uku na dokar miƙa wani kasar waje ta Najeriya ya haramta tasa ƙeyar wanda ake zargi zuwa wata ƙasa matukar yana fuskantar wata shari'ar a cikin gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa FG ta shigar da ƙarar?

Gwamnatin tarayya ta nemi izinin tura Abba Kyari zuwa ƙasar Amurka ne domin ya fuskanci tuhumar da ake masa kan zargin haɗa hannu da Ramon Abbas, wanda ya fi shahara da Hushpuppi wajen aikata damfara.

Amurka na tuhumar, Hushpuppi, da Zambar wani ɗan kasuwar ƙasar Qatar makudan kuɗi da suka kai kimanin Dala Miliyan $1.1m. Ya yi ikirarin da hannun Abba Kyari a ciki.

A watan Fabrairu, Kotun California ta umarci hukumar bincike ta ƙasar Amurka FBI ta kamo Kyari, wanda ya musanta zargin da ake masa a shafinsa na Facebook, daga baya ya goge.

Kara karanta wannan

Yar Manya Jinin Sarauta: Hotuna Da Bidiyoyin Shagalin Kamun Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero

Gwamnatin tarayya ta ofishin Akanta Janar ta shigar da bukatar mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022 da nufin samun izinin kai Kyari Amurka, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ƙarar da aka yi wa taken, 'Bukatar iza keyar Abba Kyari zuwa Amurka," na ɗauke da kwanan watan 1 ga watan Maris kuma an shigar da ita a Kotu ranar 2 ga watan Maris, 2022.

A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da baiwa Kamfanoni biyu kwangilar tsaron titin jirgin ƙasa a Abuja

Gwamnatin tarayya ta amince da ware miliyan N718.16 domin aikin tsaron Titin Jirgin kasa dake birnin tarayya Abuja.

Ministan Abuja, Muhammad Bello, ya ce an baiwa Kamfanoni biyu kwangilar ba da tsaro a layin dogon mai tsawon kilomita 45.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262