Da Alamun PDP Ta Kwace Ogun, Mabiya Tsohon Gwamna Amosun 10,000 Sun Fita Daga APC

Da Alamun PDP Ta Kwace Ogun, Mabiya Tsohon Gwamna Amosun 10,000 Sun Fita Daga APC

  • Da alamun jam'iyyar PDP ta jihar Ogun za ta maimaita abinda tayi a Osun a zaben gwamnan 2023
  • Bayan rashin AbdulKabir Akinlade wanda tuni ya koma PDP, yanzu mabiyan Sanatan APC, Amosun, sama da dubu goma sun koma PDP
  • Siyasar jihar Ogun ta sauya zani tun bayan lokacin da Amosun ya lashi takobin sai Gwamna Abiodun ya taba kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abeokuta - Dubban mambobin jam'iyyar All Progressives Congress APC a ranar Juma'a sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ogun.

Wadanda suka sauya sheka mabiya ne ga tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai ci, Ibikunle Amosun; da tsohon Gwamna Segun Osoba da tsaffin mabiyan gwamnan jihar Dapo Abiodun.

Daga cikinsu akwai tsohon mataimakin kakakin majalisa, Tola Banjo, Saka Ahmed da Yinka Asaye, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawa Da Atiku A Birtaniya, Wike, Ortom Da Ikpeazu Sun Dira A Port Harcourt

Bugu da kari akwai dan takaran gwamnan jihar a zaben 2019 karkashin LP, Modupe Sanyaolu da dukkan tsaffin Kansilolin jihar tsakanin 2016 da 2019 lokacin mulkin Amosun.

Hakazalika cikin wadanda suka sauya sheka akwai mambobin jam'iyyar Labour Party (LP), Allied Peoples Movement (APM), Peoples Redemption Party (PRP), Social Democratic Party (SDP) da African Democratic Congress (ADC).

Dukkansu sun alanta goyon bayansu ga dan takaran gwamnan PDP, Ladi Adebutu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adebutu
Da Alamun PDP Ta Kwace Ogun, Dubban Mabiya Tsohon Gwamna Amosun Sun Fita Daga APC Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Sikirulai Ogundele, da sauran jigogin jam'iyyar sun karbi bakuncin masu sauya shekan ne a hedkwatar jam'iyyar dake Abeokuta, riwayar Gazzete.

Ogundele ya musu alkawarin cewa ba zasuyi nadamr shiga PDP ba.

Dan takaran kujerar mataimakin gwamnan jihar, AbdulKabir Akinlade, yace PDP za ta lallasa APC a zaben 2023 ko shakka babu.

Shi kuma dan takaran gwamna, Ladi Adebutu, ya yi alkawarin cewa zai magance matsalar tsaro, rashin aikin yi, da kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An Bude Sakatariyar NNPP A Jihar Borno, Zulum Ya Bamu Hakuri: Kakakin Kwankwaso

Tsohon Gwamnan APC Ya Fasa-kwai, Yace da Magudi Jam’iyyarsa ta ci Zabe a 2019

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun yace Gwamna mai-ci, Dapo Abiodun ya lashe zabe a 2019 ne ta hanyar magudi da murdiya.

Punch ta ce Sanata Ibikunle Amosun ya bayyana wannan ne a lokacin da aka ba shi lambar yabo a wajen taron da kungiyar Abeokuta Club ta shirya.

A ranar Juma’a, 5 ga watan Agusta 2022, Abeokuta Club tayi bikin cika shekara 50 da kafuwa.

Ibikunle Amosun ya yi wa APC zagon-kasa a zaben gwamnan jihar Ogun a 2019, ya marawa Adekunle Akinlade baya wanda ya yi takara a inuwar APM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel